Kwanaki kadan da kisan kiyashin Zabarmari a Jihar Borno, wanda ya halaka mutane da dama kuma ya yi matukar fusata Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, gwamnan ya bayar da umurnin hana gina sabbin gidajen sayar da man fetur (PFS) a kwaryar birnin Maiduguri da kewaye.
Gwamnan ya bayyana cewa, gina-ginen da a ke yi barkatai hadi da gidajen man fetur din babbar barazana ce ga rayuka da dukiyoyin jama’a a babban birnin da yankunan karamar hukumar Jere a jihar.
Da ya ke bayyana damuwa dangane da al’amarin karshen mako a birnin Maiduguri, babban Sakataren Hukumar Tara Muhimman Bayanai kan Yanayi (BOGIS), Injiniya Adam Bababe, ya ce, yawaitar gina gidajen sayar da man a barkatai a cikin jama’a babbar barazana ce ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Bugu da kari kuma ya ce bincike a matakin farko da wani kakkarfan kwamiti ya gudanar ya nuna cewa a halin yanzu akwai sama da gidajen mai 200 a cikin birnin Maiduguri.
“Amma matsayar da mu ka cimma a yanzu, babu zancen gina sabbin gidajen man ba, saboda daga yanzu ba zamu sake bayar da takardar umurnin gina sabon gidan sayar da man fetur ba a birnin,” in ji shi.