Ya Kamata A Ci Gaba Da Ba Ronaldo Girma

142

Daga Abba Ibrahim Wada

 Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane, ya ce dan wasansu na gaba Cristiano Ronaldo na bukatar a mutunta shi sosai duk da rashin cin kwallaye da yake yi a gasar La Liga ta bana.

Zidane  ya ce ya kamata su ba wa Cristiano karin goyon baya da kuma girmamawa saboda ya cancanta ayi masa hakan

Ronaldo, mai shekaru 32, ya ci kwallaye 8 daga cikin 14 da Real ta ci a gasar zakarun Turai a wasannin rukuninsu na takwas da yahada da Tottenham da Dortmund da kuma APOEL

Dan wasan kuma ya taimaka wa Real Madrid wadda itace  zakarun gasar sau 12 sun kai matakin gaba na gasar ta zakarun turai a matsayin na biyu a rukunin nasu inda Tottenham ta kasar ingila ce a matsayi na daya.

Ba wani dan wasa da ya ci yawan kwallayen da Ronaldon ya zura a raga a gasar ta zakarun Turai, amma kuma a bana kwallo biyu kawai ya ci a gasar La Liga.

Yanzu dai duk maganganun da ake yi a Spaniya na kafin wasa ana yinsu ne a kan kamfar zura kwallon ta Ronaldo a gasar La Liga, inda maki 8 ke tsakanin Real din da Barcelona ta daya a teburin na laliga.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here