Hatsaniya ta ɓarke a kasuwar Banex da ke Wuse, Abuja, a ranar Asabar, yayin da wasu da ake zargin ƴan daba ne suka kai wa Sojoji hari.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, sai dai wani ɗan kasuwa ya ce an kai wa sojojin hari ne bayan rashin jituwa da wasu mutane a kasuwar.
- Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa
- ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Laftanar Din Soja A Yobe
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wasu samari suka yi ta cece-kuce da sojoji biyu kafin su yi rukuni rukuni su kai musu hari.
An kuma kaiwa wani mutum sanye da kayan farar hula hari a cikin bidiyon ko da yake babu tabbas ko shi soja ne, kuma an ga ƴan kasuwa suna ta kulle shagunan su domin kaucewa ramuwar gayya.
Hukumomin Soji da rundunar ƴansandan babban birnin tarayya ba su ce komai kan lamarin a cewar Daily Trust.
Kokarin jin ta bakin kakakin ƴansanda ya ci tura.
Zamu kawo muku cigaban labarin da zarar ya samu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp