Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kaduna ta cafke mutane shida da ake zargi da aikata garkuwa da mutane, tare da ƙwato makamai daga hannunsu. An samu nasarar ne sakamakon atisayen haɗin gwuiwa da ‘yansanda suka gudanar a sassan jihohin Kaduna da Zamfara.
- Tsoffin Ƴansanda Sun Fara Zanga-Zangar Ƙuncin Rayuwa A Abuja
- Edo Da Taraba : ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 31 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Musayar Wuta
Kakakin Rundunar ‘Yansanda ta Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa cewa lamarin ya samo asali ne daga wani rahoton gaggawa da wani mazaunin Ungwar Ninzom a Jagindi Tasha, ƙaramar hukumar Jama’a ya bayar ranar 22 ga Fabrairu, 2025, inda ya sanar da sace ɗansa, Hussaini Ibrahim, da wasu ‘yan bindiga suka yi.
Bayan samun rahoton, jami’an Ƴansanda daga sashin Kafanchan suka bazama don farautar masu garkuwa da mutanen. Koda yake an ce masu laifin sun tsere a farko, an ceto Hussaini daga dajin da ke kusa da yankin bayan kwana biyu, duk da cewa yana da raunin harbin bindiga a ƙafa. An ba shi kulawa a asibiti sannan aka mayar da shi ga iyalansa.
Bincike ya kai ga kama mutane huɗu: Umar Yusuf Jabiri (30), da Buhari Muhammad wanda aka fi sani da “General” (31), da Ahmadu Nasiru (51), da Zakari Saleh (50) — dukkansu mazauna Jagindi Tasha da Gidan Waya. Jami’an tsaro sun ƙwato bindiga AK-47 guda ɗaya da kuma wasu bindigogi uku ƙirar gida daga hannunsu.
A wani ci gaba kuma, bisa sahihan bayanan leƙen asiri, rundunar sashin yaƙi da garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin CSP Sani Zuntu, ta gano wani kaya mai ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da aka ɓoye cikin buhu daga Jos, Jihar Filato zuwa Gusau, Jihar Zamfara.
Hakan ya haifar da cafke Abdulmumin Sani da Naziru Musa a Gusau, inda ake zargin sun je karɓar bindigar. Rundunar ta ce za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, ya yaba da ƙwazon jami’an da suka gudanar da waɗannan atisayen tare da tabbatar wa da jama’a cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen kawar da ‘yan ta’adda daga jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp