Rundunar Ƴansandan jihar Yobe ta kama Zanaib Isa, mai shekaru 22, bisa zargin kashe mijinta mai shekaru 25, Ibrahim Yahaya, har lahira. Kwamishinan ƴansandan jihar, Garba Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan, DSP Dungus Abdulkarim ya fitar. An kama shi te na ranar 25 ga watan Yuni, 2024, bayan wani makwabcinta a unguwar Abbari, Damaturu, ya kai rahoton faruwar lamarin ga ƴansanda.
Ma’auratan dai sun samu zazzafar taƙaddama, inda har ta kai ga rigima da juna, inda ake zargin Zanaib ta daɓa wa mijinta wuƙa a kirji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Zanaib dai ta amince da kashe shi amma ta yi ikirarin cewa hakan na kare kanta ne yayin da mijin nata ke dukanta, duk da cewa ba ta daɗe da haihuwa ba. Ta kuma bayyana cewa auren nasu ya kasance mai cike da tashin hankali musamman duk lokacin da ta nemi abinci ko kuɗi.
- ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Daba Wa ‘Yar Talla Wuka A Yobe
- Jam’iyyar APC Ta Lashe Duka Kujerun Ƙananan Hukumomin Yobe
CP Ahmed ya nuna alhininsa game da faruwar lamarin kuma ya bukaci ma’auratan da ke fuskantar cin zarafi a cikin gida da su nemi taimako daga hukumomi ko shigar da ƙararraki ko tuntuɓar kotunan iyali.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su rika kula da al’amuran auratayya cikin natsuwa don hana ƙananan rikice-rikice su rikiɗa zuwa manyan har ta kai ga aikata laifuka kamar kisan kai.