Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Arewa-Maso-Yamma, Salihu Lukman, ya bayyana cewa jam’iyyun adawa da wasu shugabannin APC sun fara tattaunawa kan samar da sabuwar tafiyar siyasa kafin zaɓen 2027.
Lukman ya ce yawancin ‘yan siyasa na Nijeriya ba su yarda da tsari mai na gasar ko gogayya ba, suna fifita biyan buƙatun kansu wajen neman mulki ta hanyar danniya da maguɗi.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Za Mu Fara Zawarcin Kwankwaso – PDP
- PDP Ta Nemi Tinubu Ya Binciki N25trn Da Ake Zargin Shugabannin APC Sun Sace
A cikin sakonsa na sabuwar shekara, ya jaddada cewa shugabanni na gari ya kamata su ba wa gasar siyasa dama don tabbatar da sahihancin shugabanci a kowane mataki.
Ya kuma kira ‘yan Nijeriya su tashi tsaye don ganin an kawar da APC a 2027 tare da samar da shugabanni masu son ci gaban ƙasa. Lukman ya ce dole ne a samar da jam’iyya mai mutunta dokokinta, wadda za ta bambanta da APC, PDP, LP, NNPP da sauran jam’iyyun da ake da su.
“Samar da irin wannan jam’iyya na da wahala, amma zaɓinmu shi ne mu koma kan hanya ta siyasa da ake gogayya domin samun shugabanni na gari, tare da daina dogaro da ‘yan siyasar da suka jefa ƙasar cikin wannan hali,” in ji shi.
Lukman ya ce akwai yiwuwar Nijeriya ta gyara tsarin siyasa, ta hanyar samar da shugabanni da za su yi wa al’umma hidima, tare da mayar da ƙasar cikin jerin ƙasashe masu cigaba. Ya yi kira da a fara tunanin sabon tsarin siyasa mai ƙarfin haɗin kai da ƙwazo, domin sake fasalin Nijeriya kafin 2027.