Ɗan takarar jam’iyyar All APC, Monday Okpebholo, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar a jiya Asabar, 21 ga Satumba, 2024.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ce ta sanar da sakamakon ta hannun babban jami’in tattara sakamakon zaɓe, Farfesa Faruk Adamu Kuta, Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, a daren yau Lahadi a birnin Benin.
- Fargaba Da Ruɗani Ya Zagaye Shirin Tattara Sakamakon Zaben Gwamna A Jihar Edo
- Ko Ya Kamata Mane Ya Bar Liverpool?
Okpebholo ya samu ƙuri’u 291,667, inda ya doke babban abokin hamayyarsa daga jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, wanda ya samu ƙuri’u 247,274. Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Olumide Akpata (SAN), ya zo na uku da ƙuri’u 22,761.
Jam’iyyar APC ta lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 11 daga cikin 18 na jihar Edo, yayin da PDP ta samu rinjaye a ƙananan hukumomi 7. Jam’iyyar LP ba ta yi rinjaye a wata ƙaramar hukuma ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp