• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 weeks ago
Maulidin

Manzon Allah (SAW) rahama ne ga halitta gaba daya, da mun karanta fatiha kuma sai mu ji tana cewa “godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halitta ” ba wai Ubangijin musulmai su kadai ba. Shi “kitabu” (hukunce hukunce na Shari’a) shiriya ne ga masu tsoron Allah (hudan lil muttakiina), Amma “kur’anu” (ilmi) kuwa shi shiriya ne ga halitta (hudan linnaasi). To mungode Allah yan’uwa, wannan shi ne sakon Annabi Muhammad (SAW), mu rike wadannan abubuwa uku, mu yi ta murna a kansu; na farko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shi ne cikamakon ma’aika, na biyu sakonsa (SAW) shine cikamako; don haka dole ya bambanta da saura, sannan na uku Manzon Allah (SAW) rahma ne ga halitta; don haka komai na sa yafi sauki don ya tafi da ‘yan Adam baki daya. To mu rike wannan: idan za mu yi kira, to mu rika yin kira yadda Annabi Muhammad (SAW) yake yi, mu san wannan addini na halitta ne gaba daya ba wai iya mu kadai ba, ba wai iya wata kabila kadai ko wata kasa kadai ba.

Don haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kafa wayewa da birnantaka (cibilization and culture). Wannan ne ya sa Makkah ta kasa karbar sakon Manzon Allah (SAW) cikin hanzari ba saboda tsohon gari ne (ma’ana “ummul-kurah”), gari ne na wadansu mutane, gari ne na wata kabila (don haka akwai kabilanci a cikin garin), gari ne wanda duk abin da ka taba sai an yi maka gori a kansa. To wadannan mutane ya za a yi su yarda sabon abu ya shigo cikinsu?

  • Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (2)
  • Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

Amma mutanen Madina su kuwa mutane ne wadanda suke neman duk wani wanda zai kawo masu ci gaba a kan ya zo ya zauna a cikinsu. Sunan Garin Madina “Yathrib”, kabilu biyu ne kawai a ciki; (i) Ausu da (ii) Khazraj, sai Yahudawa; Kainuka’a da Nadhiru da Kuraizah a gefensu, amma kuma Kakarsu gaba daya guda daya ce sunanta Kailata. To Manzon Allah (SAW) sai ya ga ga wuri, amma kuma ko inda ya zauna har yanzu dai akwai kabilu, Ausu da Khazraj, akwai yiwuwar fitina, sai Manzo (SAW) ya canza mata suna daga Yathrib zuwa “Madinah” (watau Birni), su kansu kabilun ma sai ya canza masu suna suka koma “Ansaru” (ma’ana mataimaka). Yanzu da Ausu da Khazraj da duk sauran sunansa daya, watau “Ansaru”, su zauna lafiya da addini daya, gari daya.

Amma da Manzon Allah SAW ya bar su da sunan Ausu da Khazraj din nan ba za a taba zama lafiya ba. To wannan irin wayewa da Manzon Allah SAW ya nuna to haka addinin yake. Babban misali shi ne irin yadda muka hada addini da al’adar garuruwansu na Nijeriya, za ka ga da ka je Abuja komai ya fita daban, ta hanyar ‘yanci da walwala da sakewa a addini, akasin a tsofaffin biranenmu wanda da ka yi abu na addini amma bako masalan, za ka ji tsofaffi sun fara fadar: “kai dan gidan waye a garin nan? Waye babanka a garin nan?”

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo mana da wayewa da birnantaka, ya zo mana da Kur’ani, wanda yake nuna mana birnantaka shi ma, ya yarda da zaman kabilu a waje daya, ya yarda da zaman addinai a waje daya, ya yarda da zaman littafai kala-kala (kamar yadda muka kawo a tafsirai), ya yadda da zaman jama’a kala-kala; amma dai a zama ana karkashin tsarin mulki (constitution) guda daya. Shi kuwa tsarin mulki (watau constitution) ba addini ko kabila yake dubawa ba, yana duba zaman lafiyar ‘ya`yan wannan kasa ne. Wannan kuwa rahama ce, ita rahama idan ta zo babu ruwanta da addini ko kabila ko al’ada, wannan alheri ne. Muna addu’ar Allah ya dawo da dukkan Musulmi a kan hanyar Manzon Allah (SAW), mu zama rayayyu, mu guji fitintinu, mu bi wannan littafi na Manzon Allah (SAW) da ya wayar da kan duniya baki daya, ya sa musulunci ya keta duniya tun daga Sindu, watau Pakistan (duk da cewar daga baya ya shiga har Hindu, watau Indiya, da Jakarta, da sauransu) sai da ya kai har Danja (Morocco), sai da ya kai har Faransa, cikin wayewa.

LABARAI MASU NASABA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan aka bar mu sai dai halal da haram kawai! Su ma din an hana ma halal din gurbin ta, ba mu da wata magana sai dai haram! Da a ce malamai biyar za su taru, to za ka ga ba za su kago komai ba sai haram. Amma sauran malaman kasar Turai kuwa da zarar sun hadu sai ka ga sun kago wata sabuwar kira, su kuma mutanenmu sai dai ka ji sun ce “ai duk wannan duniya ce suke kagowa!”. To wa ya kai ka lahirar in ba duniyar ba? Yanzu ba don sun kago jirgin sama ba waye zai kai ka Hajji da Umrah cikin sauri?

Jama’a mu waye, saboda addininmu wayayye ne, Annabinmu wayayye ne, Kur’aninmu wayayye ne. Abin da yasa bama fadar wadansu abubuwan ma saboda raunana. Amma yanzu an waye duka gaba daya, wayar salular nan taka babban malami ce, ka tambayi “Google” ko mene ne za ta zo maka da labarin komai, duk wasu abubuwa da aka canza a addinin nan siyasa ce ta jawo aka canza shi, amma asalinsa lafiya kalau yake, duk wayewa ce da sauki da ci gaba, idan ka duba Al-kur’ani duk haka za ka gani.

Mu yi murna dai jama’a, kuma yana ga kan malamai na addini, su rika binciken gaskiya duk inda take, su rika binciken ilimi, mu koma ma manyan littafai, littafan da aka yi tun daga wajen karni na biyu, abubuwa sun faru da yawa wanda ba za su fadu ba, amma ga littafai na karni na biyu tun daga nan aka fara, malamai sun yi kokari, mu rika koma ma wadannan da wayewa da fahimta da kwakwalwa irin ta zamani ba irin ta wancan zamani ba, saboda duk abin da suka yi mai kyau ne, amma kuma an ci gaba, Allah shi ne zamani, Allah ya kawo wayewa, Allah ya kawo wadanda Annabi da kansa ya fadi zuwan zamaninsu da wayewarsu. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce “Karshen zamani ilImi zai yawaita”. Amma ikon Allah, galibin littafan da muke karantawa suna nuni da karshen zamani ilimi zai kare. Ka san babu wanda ya isa ya ce ilimi ya kare a yanzu, yanzu ilmi ya fara ma! Ka ga ashe wannan hadisi da Manzon Allah ya ce karshen zamani ilimi zai yawaita gaskiya ne kuma shi ne daga Manzon Allah (SAW), ba littafan malaman nan ba.

Don Allah malamai ku duba manyan littafai, ku zama masu amana ta ilimi (amana ilmiyya), ku zamanto masu hango ma al’umma ci gaba, da wayewa, ba masu dakikantar da al’umma ba, ku zamanto jagorori a cikin duk abin da za ku fada, da duk abinda za ku rubuta, da duk littafin da za ku yi, duk abin da kuka yi zai same ku a cikin kabarinku. Kar don wani abu bai dace da jama’arku ba ku ce karya ne, ko ku ki yarda da shi, ko bai dace da kabilarku ba, ko bai dace da kungiyar da kake bi ba. Duk wadannan sun shiga cikin addini sun lalata shi, ba laifi rike akidu da maz’habobi amma kuma ya kamata a dauki abubuwan da suke ciki masu kyau a zubar da abubuwan da ba su da kyau. Zamani ya yi fa wanda in dai ba mu gyara ba Allah zai gyara mana fa! Manzon Allah (SAW) ya yi gaskiya, mai gaskiya ne abin gaskatawa, ya isar da sako kuma ya isar da amana. Mu zama masu adalci; asali shi ne wanda zai yi hukunci a tsakanina jama’a biyu kuma ya yi adalci a tsakaninsu. Kisdu kuma shi ne a tsakanin mutum biyu kawai, misali kamar tsakanin mai awo da wanda ake wa awon.

Muna taya dukkan al’ummar musulmi murnar ganin wannan lokaci mai tarihi na cikar Manzon Allah (SAW) shekara 1500 da haihuwa. Alhamdu Lillah!

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

September 5, 2025
Next Post
Me Ake Nufi Da Ado? 

Me Ake Nufi Da Ado? 

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

October 16, 2025
Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.