Babbar kotun tarayya mai lamba 1 dake zamanta a gyaɗi gyaɗi ƙarƙashin mai shari’a M A Liman ta sanya ranar 13 ga wanna wata domin bayyana matsayinta kan hurumin sauraren ƙarar da Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar gabanta yana neman ta haramtawa majalisar dokokin jihar Kano da gwamnatin jihar rushe masarautun jihar biyar.
Gidan Radiyo Kanawa da ke Kano, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; zaman kotun na yau lauyoyin gwamnati da shugaban majalisar dokokin jihar Kano sun yiwa kotun ƙarin hasken kan batun rashin hurumin sauraren ƙarar.
- An Tsaurara Tsaro Bayan Fara Shari’a Kan Rikicin Masarautar Kano
- Mun Amince Da Sauke Mu, Ƙaddararmu Ce Haka – Sarkin Gaya
Da farko kotun ta bukaci ɓangarorin biyu su yi mata bayani kan huruminta na sauraren ƙarar inda kowanne bangare ya yi bayani tare da kafa hujjoji da irin shari’o’in da suka gabata kan rikicin masarautu a ƙasar.
Bayan sauraren doguwar mahawarar daga dukkanin ɓangarori biyun alƙalin kotun AM Liman, ya sanar da ranar da kotun za ta yanke hukunci kan wannan batu.