Farfadowar Jam’iyyar PDP: Ko Za Ta Sake Tasiri A Siyasar Nijeriya? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Farfadowar Jam’iyyar PDP: Ko Za Ta Sake Tasiri A Siyasar Nijeriya?

Published

on


An kafa jam’iyyar PDP ne a shekarar 1998; da farko a hannun kididdigaggun mutanen da basu wuce 18 ba, wadanda daga bisani yawan su ya doshi 34: wadanda suka kuma kaance sanannun mutane masu fada a ji a kasar nan da suka shafi tsoffin sojoji, ’yan kasuwa, ‘yan rajin kishin kasa da ’yan siyasa hadi da wasu daidaikun kungiyoyin al’umma da na siyasa da suka dunkule wuri guda suka narke a ciki, sai daga bisani suka yi rijista da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC). Tare da jam’iyyar APP wadda daga baya ta rikide zuwa ANPP da takwarorin su, a cikin watan Disambar shekarar 1998.

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Dangane da wadanda suka dauki nauyin goyon cikin nakuda da karbar bikin haifuwar jam’iyyar PDP sune Chief Aled Ekwueme da Alhaji Abubakar Rimi da Chief Sunday Awoniyi da Alhaji Adamu Ciroma. Sauran sun hada da Alhaji Lawal Kaita da Alhaji Sule Lamido Alhaji Atiku Abubakar da Chief Solomon Lar, irinsu Iro Alhaji Aubakar da Alhaji Dan Musa.

Haka nan ma akwai Farfesa Ango Abdullahi da Alhaji Tanko Yakasai da Ambasada Aminu Wali, Ambasada Yahaya Kwande, Farfesa Jibril Aminu, Farfesa Iya Abubakar da Alhaji Bello Kirfi. Har wala yau da mutane irin su chief Barnabas Gemade da Farfesa Daniel Saror, Dukta Sulaiman Kumo da Chief Tom Ikimi da Sanata Walid Jibril da Akhaji Bamanga Tukur, Chief Abubakar Olusola Saraki da Kanal Ahmadu Ali da makamantan su.

Tun bayan kafuwar ta a matsayin jam’iyya mai rijista, manazarta sun dauki jam’iyyar PDP tamkar wadda ta shiga fagen siyasa da kafar dama, musamman yadda take samu damar shiga gaban takwarorin ta a duk lokacin da aka shaya dagar fagen zabuka, tare da tashi da babban kaso a kusan kowanne matakin zabe (tarayya, jihohi ko kananan hukumomi); inda ta tashi da kaso hudu bisa biyar cikin zabukan da suka gudana a shekarun 1999, 2003 , 2007 da a 2011.

Wadannan kwarya-kwaryan nasarori sun samu ne kafin manyan zabukan 2015, inda kasuwar jam’iyyar PDP ta yi daren-kure, yanayin da ya jawo ta kwashi kashin ta a hannu a gamon ta da sabuwar jam’iyyar gamin-gambizar APC wadda ta tumur-mushe ta; baya ga duk da yadda ta grime ta a haife, inda aka yi nakudar APC a 2013. Duba da kuma yadda PDP ta sha alwashin cewa sai ta dauki shekaru 60 tana yi wa ’yan Nijeriya mulkin mulaka’u; kamar yadda wani jigon ta Mista Prince Bincent Ogbulafor, a shekarar 2008, ya daba kafa kasa ya ce ‘sai PDP ta mulki Nijeriya tsawon shekaru 60’.

A cikin rashin sa’a, hakar PDP ta kasa kai banten ta, ta la’akari da yadda jam’iyyar ta kasa kare kambin ta zuwa wannan dogon lokaci da ta yi hasashen kai wa; maimakon 60 sai ta tsaya 16. Duk da tun kafin wannan lokacin, manazarta sun sha bayyana cewa, bisa ga hakikanin gaskiya jam’iyyar PDP bata taba cin halastaccen zabe na kashin kanta, ba tare da magu-magu a cikin akidar ta camfin murde zabuka. Koda yake ba dole ne a ce wannan zargin yana kan gaba dari-bisa-dari ba, face dai irin wannan zargin wanda aka sha likawa PDP ya yi tasiri wajen kafuwar APC maja, a cikin watan Yulin shekarar 2013.

A hannu guda kuma, jam’iyyar PDP ta fi tabuka abin a zo a gani a mafi akasarin cikin yankuna shida (6) na kasar nan. Bayan an cire tasirin jam’iyyar AD; mai tagomashin al’ummar yankin kudu maso-yamma, sai APGA da ta mamaye tsukin yankin kudu maso-gabas. Yayin da jam’iyyar ANPP ke baje kolin ta a yankin arewa; a kebance arewa maso-yamma da arewa maso-gabas.

Cikin lokuta da dama masu bibiyar lamurran siyasar Nijeriya sun sha bayyana mabambantan ra’ayoyi dana bai-daya dangane da rashin tabbaci da sahihancin yadda jam’iyyar PDP ke murkushe abokan takara da karfin dawo-dawo a lokacin zabuka tare da zargin yiwa dokokin zaben hawan kawara. Daya daga cikin masu irin wadannan zarge-zargen a shekarun baya shi ne zakakurin marubucin nan wanda ya taba samun kyautar rubutun Adabi, Wole Soyinka, inda ya zargi jam’iyyar PDP cikin shagube mai taken “Shekar makasa” bisa duba da adadin mutanen da ke rasa rayukan su, duk lokacin da kakar babban zabe ta karato.

Dadin-dada wa kuma an sha nuna wa PDP yatsa tare da zargin kitsa tashin tashinar hargitsin bayan zabuka, domin kawai ta shafawa manyan jam’iyyun adawa kashin kaji ko rage karsashin mabiyan su. Musamman irin su AD da ANPP, kuma wannan kutunguilar siyasar PDP ce ta jawo was jam’iyyar adawa ta AD subucewar jihohin biyar cikin shida da take rike dasu a yankin Yarbawa (kudu maso-yamma) a zaben 2003.

A cikin irin wannan halin ne ya sanya jihar Legas ce kadai ta tsira a hannun Bola Ahmed Tinubu, daga irin sabat-ta-juyen aringizon da aka dade ana zargin PDP. Ita ma babbar jam’iyyar adawa ta ANPP bata tsallake halin da takwarorin ta suka fada na mamayar babbar jam’iyya mai mulki ba, saboda yadda maimakon jan-zaren ta a tsakanin jihohi bakwai a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007; yayin da ta fuskanci tutsun jihohin Zamfara a karkashin Mahmuda Shinkafi hadi da Isa Yuguda a Bauchi, wadanda PDP ta kwace bayan zaben 2007. Bugu da kari kuma da karbe iko da jihohin dake karkashin jam’iyyar PPA (Progressibe Peoples Alliance), Ikedi Ohakim a Imo da Theodore Orji na Abia.

Bisa yadda wannan halin zarmiya na jam’iyyar PDP ne ya jawo jam’iyyun adawa na wancan lolaci, cikin kowanne sa’in suke yin korafe-korafen magudi da murdiye wuyan zaben zuwa yadda Duke da muradi. Jam’iyyun sun sha bayyana yadda PDP ke amfani da kudi ko wasu hanyoyi na daban wajen sayen kananan jam’iyyun siyasa. Inda wani jikon ’yan adawar ke zargin gwamnatin PDP da amfani da yan-sanda tare wasu jami’an tsaron wajen cin zarafin wasu yan takara da almuddahanar murde zabe.

Kara wa da karau kuma, yadda PDP ta yi amfani da kungiyoyin yaki da cin hanci da karbar rrashawa na EFCC da ICPC wajen farautar yan adawa, a cikin wadannan shekaru 16 da ta dauka tana mulkin Nijeriya. Musamman kalamin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi a gabanin zaben 2007; inda a bainar jama’a aka ji shi yana cewa “wannan zaben na ko a ci ko a mutu ne” a wurin sa da jam’iyyar sa ta PDP.

Haka ko aka yi, saboda a tarihin siyasar Nijeriya ba a taba samun kazamin zabe irin na wancan shekarar ba. Wanda masu sa ido na kasa da kasa dana cikin gida, duk saida suka caccaki munin sa tare da bayyana zaben a matsayin wanda bai cika ma’aunin sikelin zabukan duniya ba; amma dai yadda aka dama shi haka aka sha shi.

Wadannan tsallen-badaken da jam’iyyar PDP ta rinka tabkawa, inda hatta ‘yan jam’iyyar basu kubuta daga kama-in-keta ba, inda a hakan ya jawo mata fadan cikin gida da rarrabuwar kawuna. Al’amarin da ya jawo PDP ta fada mummunar jinyar cuta mai karya garkuwar jiki. Musamman bayan rayuwar shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar’aduwa, inda Jonathan ya maye gurbin sa a cikin rudanin ganin cewa tunda dan kudu-Obasanjo yayi shekaru 8 dole ne a nemo wani daga arewa ya cike sauran, tare da kafa hujja da kundin tsarin jam’iyyar PDP.

Kiki-kakan da ya janyo karin rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, inda wasu daga cikin jiga-jigan ta a arewa yin tofin Allah tsine da zargin shirya munakisa a cikin kundin tsarin mulkin PDP wajen sake maido da mulkin ya koma bangaren kudanci duk da yadda yake a tsarin karba-karba; bayan Olusegun Obasanjo daga kudun ya kammala shekaru 8.

Wannan rikita-rikitar ta zafafa zukatan wasu da a cikin shekarar 2013 suka ayyana ballewa daga asalin uwar jam’iyyar inda suka kafa sabuwar PDP; baya ga yadda bahaklatsar ta tilasta ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar tare da gwamnonin jam’iyyar guda bakwai, a lokacin da jam’iyyar ke gudanar da babban taron ta na ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2013. Wanda daga cikin adadin wadannan gwamnonin akwai Chibuike Amaechi daga jihar Ribers, yayin da sauran 5 tare da mataimakin shugaban kasa daga arewa suka runtuma zuwa sabuwar jam’iyyar APC.

Yanayin da ya jawo wa jam’iyyar PDP shan mummunan kaye inda ta rasa kujerar shugabancin kasa a hannun Mista Goodluck Johnathan, hadi da kaso mai yawa a zaurukan majalisun tarayya da asarar kujerun gwamnoni masu yawa zuwa ga sabuwar jam’iyyar APC. Inda ana iya cewa, kenan mafarkin PDP na mulkar Nijeriya tsawon shekaru 60 ya koma yaudarar kai?

Bugu da kari kuma, masu nazari sun tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta tadiye kan ta ne; saboda shugaban kasa Muhammad Buhari ba ya zo wa ‘yan Nijeriya da wani bakon abu bane da ya saba da na lokutan baya a yunkurin sa na hawa karagar mulki, PDP ce da kanta ta shatale kafafu. Kuma hakan ya faru ne ta dalilin rashin tabuka abin a zo a gani da rashin gaskiya da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar; cutar da sakamakon ta bai bayyana ba sai a wannan jikon, a shekarar 2015.

Jam’iyyar PDP A Bayan Taron Fatakwal

Rashin tabbas ya bayyana dangane da inda alkiblar jam’iyyar ta dosa tun bayan gudanar da babban taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP; wanda ya gudana a birnin Fatakwal tare wanda a cikinsa aka nada Sanata Ahmed Makarfi a matsayin shugaban kwamitin rikon-kwarya. Wannan kwamiti dake karkashin Makarfi ya rika kai-gwauro da mari a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar, a wajen babbar sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

A hannu guda kuma, Sanata Ali Modu Sheriff, ya yi tsayin gwamnin-jaki tare da ikirarin cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar baya ga korafe-korafen da ya rika yi dangane da yadda wasu ke yi wa kujerar tasa barazana.

A wani yunkuri na bai-daya ne Ali Sheriff da masu mara masa baya, tsohon babban sakataren jam’iyyar na kasa Farfesa Wale Oladipo, da mai binciken kudin jam’iyyar Alhaji Adewole Adeyanju, suka kutsa kai da karfin tuwo domin hawa kan kujerun su a babbar sakatariyar jam’iyyar; a matsayin su na halastattun shugabanin PDP.

 

Kai-komon da Ali Modu Sheriff ya rika yi a babbar sakatariyar jam’iyyar; masu cike da samun turjiyar jami’an tsaron ‘yan sanda, inda a karshe ya dira a wajen tare da dimbin magoya bayan sa, kana kuma ya bayyana wa manema labarai cewar ya zo sakatariyar ne a matsayin wanda babbar kotun Legas (Lagos High Court) ta tabbatar wa da kujerar har zuwa shekarar 2018.

 

Wannan matakin tare da yadda Sheriff ya dare kan kujerar ya kara ruruta zaman tankiya da ake dashi a tsakanin masu ruwa da tsaki a sha’anin jam’iyyar. Alhalin kuma Modu Sheriff ya kekasa kasa kan cewa shi ne jagoran tafiyar. Inda karawa da karau ma ya ce, ba fa shi ne da kan sa bane ya nada kan sa ba a matsayin shugaba ba. Ya nusar da cewa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ne suka tilasta masa da ya zo ya karbi shugabancin jam’iyyar, kuma ta yaya ne ake kokarin mayar dashi a-huhun-ma’ahu a sha’anin siyasa, duk da sanin kowa ne shi ba dan-dagajin ta bane.

 

Ikirarin Ali Modu Sheriff ya on na cewa baki dayan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da suka kunshi yan kwamitin zartaswa na kasa (NWC) da kungiyar gwamnonin jam’iyyar sine suka tattaru suka nemi da ya zo ya rike shugancin jam’iyyar. Ya ce sune fa; su yan kwamitin zartaswa na kasa da kwamitin amintattu hadi da kungiyar gwamnonin jam’iyyar suka mara masa baya tare da jefa masa kuri’u kaso 69 a cikin dari.

 

Kasa da kwanaki biyu da shigar Sheriff sakatariyar jam’iyyar ne sai wata tawagar matasan jam’iyyar ta shirya zanga-zanga da nufin yin watsi dashi a matsayin shugaban PDP. Yunkurin da ake kyautata zaton cewa na wata sabuwar kungiyar sake farfado da jam’iyyar ne ta jagorance shi da ake kira da PDP National Rebirth Group da PDP ‘Concerned Rescue Group’, wadanda suka mamaye sakatariyar da safiyar wata laraba.

 

Yunkurin wanda ya kai ga garkame sakatariyar jam’iyyar tare da damka makullan ga shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Walid Jibrin; wanda ya isa wajen jim kayan masu zanga-zangar sun mamaye sakatariyar da shida masu mara mashi baya. Yayin da wasu ke jingina wannan takakkar da bangaren Ahmed Makarfi. Haka zalika, da korafe-korafen da bangaren na Makarfi suka rinka yi kan cewa jami’an tsaron farin kaya na SSS ne ke marawa Sheriff baya a zakalkalewar sa a shugabancin jam’iyyar.

 

A haka wannan kai-gwauro-mari ya ci gaba tsakanin Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi, ta hanyar zuwa gaban kotuna daban-daban kana da zargin zuna tare da kalaman yarfe na siyasa iri-iri inda a karshe kotun koli ta tabbatar wa Makarfi nasara kan Ali Sheriff.

 

Baya ga hakan ne, a cikin yan kwanakin nan rahotani suka rinka yawo kan cewa an hango Sanata Ali Modu Sheriff a kofar ofis din mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osimbajo da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC. Labaran sun tabbatar da yin ganawar sirri a tsakanin Ali Sheriff da bangaren fadar shugaban kasa. Wanda kuma hakan ke nuni da cewa, da walakin; wai goro a miya.

 

Har wala yau kuma, shin wannan yana bayyana cewa Sanata Ali Modu Sheriff zai koma jam’iyyar APC ne? Idan kuma wannan hasashe ya tabbata, yaya al’amarin zai kasance; saboda zaman damisa biyu a fage daya, akwai jan aiki.Masu kula da lamurra sun bayyana cewa ajin farko bayan gwamnati karkashin jagorancin PDP al’amurra suka kara sukurkucewa a kasar nan. Saboda yadda yake taskace a kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, wanda ya tanadar wa kowanne dan kasa walwala da gudanar da rayuwar sa cikin tsanaki. Yayin da PDP ta zo sai ta rakabe da wannan damar tare da daukar alkawurran yaudarar bin kundin ta fuskacin samar da zaman lafiya da tsaro, ilimi, kiwon lafiya da kyautata wautar lantarki da inganta yanayin tattalin arziki da yin adalci wajen raba shi. Amma me ya faru cikin kasa ga shekara guda, kana a bayan kammala shekaru 16 tana mulkar yan Nijeriya?

Ko shakka babu, tsarin mulkin dimokuradiyya ya tanadi yanci da walwala ga yan kasa; daidaikun su da ayarin su, kana da tsammanin samun kyautatuwar yanayin rayuwar al’umma. Amma abin mamaki wannan ya tsaya a takarda da baki, ba a aikace ba, inda gazawar gwamnatin PDP ta bayyana karara. Yayin da yan siyasa suka kasance tamkar allolin-Misra a tsakanin talaka, inda babban abinda ya daurewa manazarta kai shi ne yadda zababbu suka yi batan-dabo a idon wadanda suka zabe su, kuma kan kace kwabo miskinan yan siyasar sun zama hamshakan masu kudi na mamaki, tare da maida din hanci da karbar rashawa tamkar wata halastaciyar harka.

Bahallatsar rib-da-ciki kan baitil-malin al’umma ya jawo ya bushewar sa karaf, ta dalilin wa-ka-ci-wa-ka-tashi da dukiyar kasa, alhalin ninkin-baninkin yan kasa na fama da tsananin talauci da kuncin rayuwa. Halin da ya jawo al’amurra suka rinka ja da baya tare da jefa kasa cikin halin ni’ya su.

Daya daga cikin tambayoyin da ke kai-kawo a zukatan ‘yan Nijeriya dangane da yadda shekarar gudanar da babban zabe ke karatowa na 2019. Shin ko ’yan Nijeriya zasu sake shiga inwar lemar PDP a wannan babban zabe mai zuwa? Koba komai dai akwai hasashen cewar rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar zai yi wuya ya bari su sake samun wata damar shan inwa guda, ballantana karbar goriba a hannun kuturu.

Kari a kan wannan kuma, inda gizo ke sakar shi ne yadda zaman doya da man-ja; ta dalilin kama-karya da jam’iyyar PDP ta rinka yi a lokacin zabukan sharar fage a jihohin kasar nan shima abin lura ne dangane da samun mutanen da zasu yi gigin fitowa a yagaggiyar lemar. A bangare guda kuma, masu hasashe sun bayyana cewa kawowa yanzu PDP ta zama kura; wadda sunan ta ya riga ya baci tun tana yarinya.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!