Connect with us

LABARAI

Abin Da Ke Kawo Cutar Ƙyandar Biri -Minista

Published

on


Daga Idris Aliyu Daudawa, Abuja

Gwamanatin tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa na wani rahoto, mai nuna cewar barkewar annobar ƙyandar Biri, a wasu sassa na ƙasa, abin ya auku ne, bayan da aka yi allura ƙyauta, da ake zargin gwamnatin tarayya ta yi.

Ministan ya musanta zargin inda yace, yana tsammanin ita wannan cuta a na kamuwa da ita ne a sanadiyyar cin naman Biri.

A sanarwar da aka fitar a Abuja ranar Lahadi, ministan yaɗa labarai Lai Muhammed ya ce ‘yan Nijeriya su yi watsi da wannan jita-jitar, wadda a cewar shi, ’yan gaza gani ne suke neman su kawo ruɗani cikin al’umma. Sanarwar dai wani mataimakin Minista ne na musamman ya sa ma hannu.

Sanarwar da ƙara jaddada cewa ba kamar yadda ake ta yaɗa jita jita ba, gwamnatin tarayya  ba ta yi, wata allurer rigakafi ƙyauta ba, a Bayelsa ko Riɓers ba, kamar yadda ake baza rahotannin ƙarya. Don haka wannan ba zai kuma kasancewa samadiyar ɓullar ƙyandar Biri ba a duka jihohin.

Ita dai ƙyandar Biri wata ƙwayar cuta  ce, da ake samu daga Birai, wadda kuma da akwai wahala a same ta ajikin ɗan adam. Ta yi kama da ta ‘yan rani ko ƙyanda.

Ministan ya bada tabbacin duk matakan da suka kamata a ɗauka an ɗauka, saboda a hana ita cutar yaɗuwa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI