Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Matasa Biyu Sun Tsalleke Rijiya Da Baya Sakamakon Ruftawar Bishiya A Bauchi

Published

on

Wasu matasa biyu sun tsallake rijiya da baya a sakamakon fadowar da wata bishiya ta yi a kansu a cikin garin Bauchi.

Lamarin faduwar bishiyar ya auku ne shekaran jiya da misalin karfe 12:00 na rana.

Ita wannan bishiyar dai ta madaci ta fadi ne a daidai layin Ahmadu Bello da ke cikin Bauchi, inda kuma a bisa tsautsayi bishiyar ta kuskuri mutane biyu; inda daya daga cikin wadanda tsautsayin ta rufta musu aka wuce da shi asibiti ranga-ranga a yayin da dayan kuma da dan saukin ciwon da ya samu.

Wakilinmu ya bankado cewa bishiyar ta fadi ne a daidai ofishin ‘yan jarida da ke Bauchi, ta kuma fadi ne a sakamakon kunna wuta domin kona ciyayi da wani wanda ba a san ko waye ba ya yi, lamarin da ya yi ta cin bishiyar sannu a hankali.

Daya daga cikin matasan da tsautsayin ya illata, kuma wanda Allah ya kubutar da shi mai suna Mu’azu Salihu ya yi bayanin yadda bishiyar ta kuskuresu “Na dawo daga makaranta, domin ni dalibi ne a jami’ar ATBU da ke Bauchi, ina hanya a sakamakon rokona da wani abokina ya yi na in rage masa hanya daga makaranta, muna zuwa daidai wajen da bishiyar ta yi sai kawai muka ji mu a kasan bishiya yashe a kan kwalta,”

Ya ce kafin kiftawa da bismilla sun gansu ruf a kasa “Zan ce Alhamdullah na gode wa Allah, wallahi in ka ga yadda mashin dina ta lallace kai abun ba magana, mun taki sa’a sosai, domin da bishiyar nan ta samemu sosai da sai dai yadda Allah ya so,”

Ya kara da cewa “Muna tashi sai mu ga a gidin bishiyar ashe an sanya wuta ne, tana ci a sannu a hankali har ta kafar da bishiyar,” A cewar shi.

Mu’azu Salihu sai ya daura laifin wa hukumar da ke kula da sha’anin shukoki da kuma bishiyoyi na jihar Bauchi “Ma’aikatar kare muhalli da albarkatun kasa ita ce ke da alhakin bibiyar bishiyoyi da kuma duba lafiyarsu, don haka sakacinsu ne ya janyo wannan lamarin,” A cewarsa.

Manema labaru sun nemi Daraktan da ke kula da bishiyoyi da shuke-suke na ma’aikatar da ke kula da shuke-suke da albarkatun kasa wato ‘Ministry of Enbironment and solid Minerals’ ta jihar Bauchi, James Dallah Sam, wanda kuma ya yi bayanin yadda lamarin ya auku.

Sam ya ce wannan bishiyar ta fadi ne a sakamakon sanya mata wuta da wani wanda har zuwa yanzu ba su kai ga gano shi ba; da nufin kona ciyayin da suke kusa da inda bishiyar take.

Haka kuma ya kada cewa, bishiyar ta madaci ta yi tsufan da jikinta babu karfin da za su iya jure wannan wutar don haka ne ta fadi “bishiyar ta tsufa sosai, da a ce jijiyoyinta basu gaji ba, wutar ba zai iya mata illa har ya kayar da ita ba,”.

Dangane da yawaitar samun fadin bishiyoyi da ake yi a cikin Bauchi, don ko a shekarar da ta gabata ma a wawajen damina, wasu jerin biya sama da bakwai sun fadi a unguwar Bauchi Club wanda har hakan ya janyoyi asara da kuma lalata dukiyoyi.

A don haka ne Daraktan shuke-shuken, James Dallah Sam ya bayyana cewar tuni gwamnatin jihar Bauchi ta tashi tsaye domin shawo kan wannan matsalar, “a lokacin da aka samu fadin bishiyoyi a yankin Bauchi Club, tuni gwamnati ta bamu umurnin mu je mu lura da dukkanin bishiyoyin da suka tsufa, wadanda reshensu ya fi karfin jijiyoyinsu domin kariya daga fadowa kan mutune ko dukiyoyinsu.”

Ya kara da cewa, “Ma’aikatarmu ta fitar da wani tsarin da za a mu domin magance wannan matsalar, yanzu haka za mu fara rage reshe-reshen bishiyoyin da suka tsufa, daga baya kuma za mu sanya wasu sabbin shukokin a gefen kowace bishiya, da zarar bishiyar ta taso sai mu yanke wancan tsohuwar kun ga mun yi sauyi kenan, ba tare kuma da amfanin da bishiyoyi ke yi wa Allah ya ragu ba,”

Ya kuma yi bayanin cewar za su sanya sabbin shukoki na zamani domin shawo kan yawaitar fadin bishiyoyi a jihar “Sannan kuma mun sanar da al’umman jihar nan kan cewar duk wanda yake fargabar bishiyar kofar gidansa ko na gidansa ta yi rassa da dama wadanda yake fargabar fadi mun ce a zo a kawo mana rahoton hakan za mu je domin sarewa,” A cewar Sam.

Wani wanda bishiyar ta fado a kan idonsa ya mai suna Muhammadu Mai Nama ya bayyana cewar “muna zaune a gefen titin kawai sai mu ga bishiyar ta fado kasa, babu wanda ya tsammaci za ta fado, sannan kuma in ka kura kan titi ne a bishiyar ta fado don haka Allah ya yi matukar taimakon domin kuwa da ba din kiyayewar Allah ba da jama’a da dama sun illata,”

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: