An bude Kwalejin Asshaheed Kauwasu A Kano — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An bude Kwalejin Asshaheed Kauwasu A Kano

Published

on


 

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya jagoranci bude Makarantar Assheed Aliyu Kauwasu wacce aka bude don zurfafa bincike da Ilimin Addinin Musulunci a karkashin shugabancin Sheik Askiya Nasiru Kabara wacce za ta koyar da Ilimin Addini a matakin Babbar Sakandare ga dalibai da suka cancanci shiga wannan makaranta wacce take Unguwar Daurawar Titin Maiduguri dake Kano.

A Jawabinsa, mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya bayyana muhimmancin neman Ilimin addini dama sauran ilimi wanda zai amfani dan adam a rayuwarsa ta duniya da kuma ta gobe kiyama inda kuma ya bayyana matsayin ilimin addini da cewa babu wani abu da zai warware kowacce irin matsala, sai ilimi don haka ya umarci al’umma Maza da Mata akan jajircewa wajan neman ilimi da aiki da shi a ko yaushe.

Shi ma Daraktan Makarantar Malam Askiya ya bayyana cewa ganin irin bukatar da al’umma take da shi a wannan zamani na ilimi da kuma yadda nauyi yama Hukumomi yawa ya sa su ma suka ga ya wajaba su fito su kara kaimi wajan bada gudun mawar su dan ilmantar da al’umma kamar yadda ya kamata kuma wannan Makaranta daliban ta sun fito ne daga sassa daban daban na Kasan nan harma da Kasashen makwamtan mu kuma Karatun za a yi shine kyauta ba tare da biyan kudin makaranta ba duk da kasancewar wannan makaranta ta kwana ne.

Ita dai wannan Makaranta dake karkashin kulawar cibiyar binciken ilimi ta Sheik Nasiru Kabara wato Nasiru Kabara Center Of Research dake Kano Makarantar ta samu amincewa daga Hukumomin masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi kuma hadin gwiwa ne da cibiyar bunkasa ilimi ta IDDEF domin dai bunkasar ilimi a tsakanin al’umma Sarkin Kano ne dai ya jagoranci bude wannan Kwaleji da ke Kano.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!