Balahirar Ciwon Hanta A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Balahirar Ciwon Hanta A Nijeriya

Published

on


Ciwon hanta ya kasance a sahun gaba cikin jerin cututtuka da ke halaka mutane farad daya musamman a lokacin da abin ya ta’azzara a jikin Dan Adam walau ya san ya kamu ko bai sani ba.

Ciwo ne da ke kama hantar mutum ya lalata sannan illarsa ta ninka ciwon kanjamau (HIB/AIDS) sau hudu kamar yadda masana suka bayyana. Likitoci sun kasa cutar zuwa nau’o’i hudu, akwai nau’in A da B da C da kuma E.

An fi kamuwa da Nau’o’in A da E ta hanyar abinci ko ruwan sha mara tsafta. Alamomin kamuwa da su sun hada da zazzabi, zawo, zafin jiki da ba a saba ji ba kana ido ya rine ya koma ruwan kwai. Su kuwa nau’o’in B da C da kuma D mutum na iya kamuwa da su ba tare da sun bayyana a fili baro-baro ba, amma za su rika cin hanta sannu a hankali har a kai matakin da ba za a iya magancewa ba.

A cewar Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Isaac Adewale ‘Yan Nijeriya milyan 20 sun kamu da mugun ciwon na hanta.

Daga cikin al’ummar Jihar Kano milyan 10 (kamar yadda yake a kidayar jama’a ta shekarar 2006), kimanin kashi 20 a cikin 100 sun kamu da cutar wanda wannan yana nufin mutum kimanin mutum milyan daya sun harbu kuma suna fama da ciwon hanta a Kano kawai!. A Jihar Benuwai kuma, an yi amannar cewa daga cikin al’ummar jihar milyan hudu (a kidayar shekarar 2016), mutum dubu dari biyar da tamanin da shida (586,000) suna dauke da cutar nau’in B. Jihar Legas wadda aka ce ita ce ta biyu a yawan jama’a a kasar nan, ita ma ba ta tsira ba kasancewar kashi 7 a cikin 100 na yawan al’ummarta sun kamu da cutar. Jadawalin bayanan kiwon lafiya ya bayyana cewa nau’in ciwon da ya fi halaka jama’a na B shi ne ya fi bazuwa a yankin Arewacin kasar nan in ban da Jihar Kwara wacce nau’in C ya fi yawa a cikinta.

Likitoci sun yi bayanin cewa za a iya warkar da cutar nau’in A cikin sauki matukar an kiyaye tsaftar abinci daga barin kazanta. Har ila yau, bayanan likitoci sun nuna cewa mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar kan tsinci kansu cikin matsanancin rashin lafiya lokacin da suke ganiyarsu ta rayuwa kamar dab da cika shekara 30 ko farko-farkon cika shekara 30 da doriya da kuma lokacin da suka cika shekara 40 da doriya.

Baya ga illoli na ciwon jiki da kisa da cutar take yi, har ila yau tana shafar cigaban zamantakewa da tattalin arzikin yankin na Arewa inda wani bincike ya gano cewa matasan yankin bila’adadin sun kasa tsallake gwajin shiga rundunonin tsaro na kasa a lokuta daban-daban saboda sun harbu da kwayoyin cutar ta hanta.

Da yake karin haske ga jaridar Daily Trust a game da ciwon, wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Dakta Yusuf Maisuna Abdulkadir ya ce mutane ba su zuwa asibiti a lokacin da suke farkon kamuwa da ciwon, a maimakon haka sun gwammace yin maganin gargajiya ko shan kwayoyin paracetamol don samun sauki wadda a cewarsa hakan kan janyo kin kawo mutum asibiti sai hantarsa ta riga ta yi mugun lalacewa. Likitan ya ce wani lokacin akan kawo masu ciwon suna amai ko zubar da jini ko kuma a galabaice.

Ita ma wata kwararriyar likita a Asibitin Koyarwa na Legas, Dakta Dabwar ta shaida wa jaridar cewa ba a cika samun nau’in D na cutar ba a Nijeriya, inda ta kara da cewa nau’in D na cutar ba zai iya haifuwa da kansa ba, yana bulla ne a lokacin da aka kamu da nau’in B.

Wakazalika, daya daga cikin sharrin cutar shi ne ba ta tashi bayyana sai ta kai matakin da ba za a iya shawo kanta ba a wani lokacin. Hakazalika, mutane da dama za su iya kamuwa da cutar ba su sani ba, za su cigaba da harkokinsu suna watayawa amma cutar na cin su sannu a hankali.

Bisa la’akari da halin-ko-in-kula da galibin ‘Yan Nijeriya musamman al’ummarmu ta Arewa ke nunawa a kan batun kiwon lafiyarsu, dole ne ciwon hantar ya rika kashe mutane tare da yadawa ga wasu. Yanayin tsarin kiwon lafiyar kasar ma abin dubawa ne ta yadda gwamanatoci ba su ba da kulawar da ta dace kan inganta lafiyar ‘yan kasa. Matsalolin da suka jibanci karancin kayan aiki, rashin isassun kwararrun likitoci da munanan dabi’un likitoci ga marasa lafiya duk sun taru sun yi wa sashen kiwon lafiyar kasar katutu. Sannan ‘yan kasa da yawa ba su damu da zuwa asibiti a duba lafiyarsu ba idan sun ji alamun kamuwa da rashin lafiya sai abin ya ta’azzara wanda wannan yana taimakawa wurin yada cututtuka masu saurin halaka jama’a kamar ciwon hanta da sauran dangoginta.

Cutar ta zama wani bala’i a cikin al’umma da ke bukatar matakin gaggawa wajen shawo kanta kamar yadda aka yi a sa’ilin da aka samu barkewar cutar Ibola a ‘yan shekarun da suka gabata saboda hatsarinta. Kar a bari sai rabin ‘yan kasa sun kamu kafin a ce za a dauki mataki.

Matakin da mutane za su dauka domin rigakafin kamuwa da ciwon hanta su ne, da farko kowa ya je a gwada shi ya tabbatar da matsayinsa; ya kamu ko bai kamu ba; wadanda suka kamu a fara yi musu magani da wuri; wadanda ba su kamu ba su yi allurar rigakafi musamman idan wani a cikin iyali ya kamu da cutar, kasancewar kwayoyin cutar suna iya rayuwa a inda jinin mai cutar ya diga na tsawon fiye da minti goma. Sannan a rika kula da wanke hannu a kai-a kai. A tabbatar da yi wa yara rigakafin cutar a duk lokacin da aka kai su rigakafin da aka saba yi wa yara. Bugu da kari, gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma su kara azamar wayar da kan al’umma game da cutar. Wannan zai taimaka gaya wajen rage yaduwar cutar da kuma magance ta da wuri ga wadanda suka kamu.

Advertisement
Click to comment

labarai