Hukumar Kula Da Tsarin Birane Ta Katsina Ta Rufe Babban Ofishin GLO — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hukumar Kula Da Tsarin Birane Ta Katsina Ta Rufe Babban Ofishin GLO

Published

on


Hukumar kula da tsara gundumomi da birane ta jihar Katsina ta rufe babban ofishin kamfanin sadarwa na GLO dake nan Katsina saboda rashin biyan haraji.

Babban Manajan na hukumar Alhaji Nadada wanda ya yi ma manema labarai dan takaitaccen bayani bayan rufe GLO dake police compound Katsina, ya bayyana cewa sun dakatar da aiki a wurin ne saboda gazawar kamfanin wajen biyan kudaden haya dana haraji.

Alhaji Usman Nadada ya bayyana cewa kamfanin sadarwar na GLO ya gaza biyan kudaden haraji na jihar Katsina da kananan hukumomi da suka tasamma naira miliyan dari hudu tsawon shekaru (4) da suka gabata.

Ya bayyana cewa matakin da hukumar ta dauka umarni ne, daga gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.

Alhaji Usman Nadada ya ce, kafin hukumar ta dauki matakin, sun aiwatar da wani taron manema labarai inda suka yi kira ga dukkanin kamfanin sadarwa da su zo su biya kudaden haraji.

Janaral Manaja, hukumar kula da tsara birane ya ce rashin gazawar da kamfanin ya yi na biyan haraji indai har kamfanin bai dauki mataki to haka zai sa gwamnati ta dauki wani kwakkwaran mataki.

Ya ma kalubalanci kamfanin na GLO na rashin gazawarsa wajen aiwatar da wasu ayyuka da zasu inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina ya bayyana godiyarsa ga sauran kamfanonin sadarwa kamar su kamfanin sadarwa kamar su kamfanin sadarwa na AITEL dana MTN wadanda ke biyan kudaden harajinsu yadda ya dace da kuma aiwatar da wasu ayyuka na cigaban al’umma.

Wakilin mu ya ruwaito cewa said a jami’an tsaro suka taso koyar ma’aikatan babban ofishin kamfanin na GLO dake K/Kaura wajen katin rufe ofishin.

Wanda tuni hukumar da abin ya shafa na kulawa da kamfanonin a jihar Katsina har sun tura abin ga gwamnatin jihar Katsina.

Alhaji Usman Nadada shi ne ya bada tabbacin hakan ga manema labarai.

Janaral Manajan ya ce hukumar tashi ta tashi tsaye haikan don gano duk masu irin wannan al’umma da hanan a ko’ina a cikin jihar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai