Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wani Direba Ya Kashe Kansa Don Ya Kasa Biyan Bashi A Ondo

Published

on

Ana zargin wani direban motar haya mai suna, Ayokunle, da kashe kansa a Anguwar Oke Ibukun, ta garin Ondo, da ke Jihar Ondo.

A cewar wata majiya, an sami Ayokunle, ne a mace ranar Asabar a dakin sa, inda ake zargin ya kashe kansa ne ta hanyar shan guba, bayan da ya kasa biyan bashin da ya ci daga wata cibiyar bayar da basuka.

Majiyar ta ce, mamacin yana daga cikin shugabannin kungiyar direbobi ta, ‘Road Transport Employers Association of Nigeria,’ a garin.

Wani wakili a cikin kungiyar wanda bai soa ambaci sunansa ba, ya ce, ya ga mamacin kwana daya kafin mutuwar na shi, ya kara da cewa kowa a Anguwar yana mamakin kashe kanshi din da ya yi.

Ya ce, “Mun yi mamakin jin ya mutuwar na shi a ranar Asabar. Na gan shi ranar Juma’a, ba wani alamun mutuwar sa a ranar Asabar, abin da bakanta rai.”

Da aka tuntube shi, Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar ta Ondo, Mista Femi Joseph, ya ce ba a kawo masu rahoton aukuwar lamarin ba.

“Na tuntubi dukkanin Ofisoshinmu na ‘yan sanda da ke nan cikin garin na Ondo, duk sun ce ba a kawo ma su rahoton aukuwar lamarin ba,” in ji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: