Mallam Bahaushe Ga Naka (I) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Mallam Bahaushe Ga Naka (I)

Published

on


07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Babi Na farko: Cabalin Cababa

 

Juma’a da dare, ga lullumi, ga iska na kadawa. ‘Yar matsakaiciyar kasuwar dare ta sayar da abinci a unguwar Tudun Galadima da ke cikin birnin ta dauki harama, ta dinkire da mutane marasa galihu; da ‘yan gari da ‘yan kama-wuri-zauna da kuma zauna-gari-banza da ma bakin haure. Ko’ina hayaniyar ‘yammata balagaggu ka ke ji: ‘a zo a sayi tuwo, a zo a sayi ganda, a zo a sayi tako, a zo a sayi kalallaba, Malam zo ga shaye-shaye da miya’. Nan ga samari masu neman ‘yammata, su ba ma cin abinci su ka zo yi ba, can gefe ga guruf na ‘yan garuwa kowa na jiran a kawo masa abin kusa da baki, can gefe ga bataliyar ‘yammata da su ba ma tallar su ka zo yi ba, sun fito yawon banza, ana ta digimi. Kowacce na rike da wayar salula. Akasarin ‘yammatan ba su yi shigar kirki ba, suturun da su ka sanya na bayyana sura ko sigar jikunnansu. Ga hantsa waje, ga shi kowacce ta sha hoda, sun kuma labta ma lebbansu janbakin-Aliya, kai ka ce ‘yan bori ne. Su na ta surutu, fadi banza fadi wofi. Wasu ma na ta fadin maganganun banza na batsa a tsakanin samarinsu.

Turai na a wurin tsaye, ta na ta raba idanu kamar amaryar karya, ta na neman Abdallah, dan yayarta, da ya fito daga gida ba a sani ba. Ta na tsaye ta na sanye da farin hijabi, ta na ta kallon yanda ‘yan Duniya ke ta surutan banza, marasa kangado. ‘Allah wadaran naka ya lalace’, ta ayyana a cikin zuciyarta. Ta yi kokarin kai kallonta ga wata ballagaza kuma, wadda ke tsaye da wani saurayi kamar za ta afka masa. Ta yi tsaki, ta karkace ta tofar da yawu. Ta kuma sake kai kallonta ga wata budurwa da ke nan zaune da farantin goro a gabanta, amma kusan kirjinta waje don ba abin da ta sa ta rufe shi. Turai ta yi tsaki. Ta kuma waiga bayanta ta kallo saitin garejin motocin J5 da ke tsallake, can ma ta ga wasu jerin samari karnukan mota kuma bakin haure, su na ta kokowa da junansu. Wuri dai ba tsari, ba doka. Kowa sake, kuma ba galihu. Baturiya ta yi ajiyar zuciya, sannan ta yi nadamar ma zuwa wurin kurum don neman yaro. Amma wannan duk bai ba ta takaici ba ma sai da ta hangi Gaje, makwabciyar yayarta ta na zaune da bangajin tuwon dawa, tuwon ma na datsa a gabanta da miyar tafashi-kada, amma ta na ta surutan banza na batsa ita da wani matashi. Turai ta nisa ta ce ‘lallai, kayan ruwa na mai guga ne, in ji masu iya magana’. Ita Gaje, ba ta ganta ba don ba ta yi tsammanin za ta gan ta a irin wannan wurin ba. Har ta ji Gaje na ta nanata ma saurayin nan wata kalma: ‘ka ba ni dankunne na tun mu na mu biyu, tun ba a ji mu ba’. Shi kuma ya na ce mata ‘sai kin zo dakin da kan ki ki dauka inda ki ka ajiye shi, tunda dakin ba bakon ki ba ne’ Wannan ya tabbatar wa Turai cewa Fati na zuwa dakunan samari, saboda mai cin goro shi ya san darajar algarara, in ji diyan Bawo.

Ta zabura ta koma gida da sauri ta na tafe ta na sallallami, ta ga abin da ya bata mata rai. Halisa yayarta ta tambaye ta ko lafiya? Ta kwashe abinda ta gano a kasuwar tuwon dare ta unguwar ta fadi mata, ta kuma yi tariyar abin da ta sha samun labara, cewa talaka ba kasafai ya ke mai biyayya ga Allah da kuma dokar kasa ba, musamman sabili da talauci dan uwan kafirci ne. Halisa ta ce mata ‘ai in dai ‘yammatan Kantuk ne kadan ma ki ka gani, ita kuma Gaje, ai ke ce ba ki santa ba, bara har cikin shege aka zubda mata, karewa kenan’. ‘Zancen zuwa dakunan samari kuma ai uwarta Atika mai tuwo ta sani har dakunan samarin ta ke ma kwana. Duk a kan idanunmu ake komi’, cewar Halisa. Turai ta tuma da al’ajabi, ta na ganin Gaje kamar ko an sanya mata hannu a baki ba ta iya cizawa. Jin wannan labarin ya sanya gabanta ma ya fara faduwa kamar ana kwada mata guduma. Bayan gama tunani tare da yin Allah wadarai, sai ta sungumi buta ta yi alwallah ta yi sallahr isha’I, sannan ta dauki Alkur’ani ta yi karatu, wanda ya kaita har karfe goma na dare.

Turai fara ce tas, kyakykyawa, mai matsakaicin tsayi, ta na da hanci mai tsayi.  Zagayayyar fuskarta ita ta nuna daga jinsin fulanin yamma ta fito. Ta na da shiru-shiru ko rashin kwaramniya. Sai ku kwashe awoyi a wuri tare da ita ba ka ji bakinta ba, sai ma ka dauka cewa kurma ce. Ta na da yawan son karatun Alkur’ani mai tsarki. Tabi’ar ta dai irin ta Larabawa. Ta na da rayuwa mai tsari, don a kowanne wakati da abin da za ta yi, ba ta zaman banza.  Za a iya ajiye ta a shekaru kimanin ashirin da hudu. Rabon ta da kasar Langeri tun ta na ‘yar shekara biyar da haihuwa, sa’ilin da kanwar mahaifiyarta ta tafi Misra tare da ita. Daga can kuma wanu kanen mahaifinta ya wuce da ita Amerika. Don haka da birnin Katine da lafira Turai ba ta san ko daya ba, kafin wannan lokacin. A can Amurka ta yi karatun Elementare, ta shiga babbar makaranta, sannan ta yi kwaleji, ta zarce Jami’a. A Jami’ar Kalifoniya Turai ta yi karatun digiri na farko a fannin halayyar Dan Adam. Sannan bara kuma ta fara karatun digiri mai daraja ta biyu, duk a kan nazarin halayyar Dan Adam a dai nan Jami’ar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai