Za Mu Hada Kai Da Gwamnoni Domin Yakar Shaye-Shaye - Bala Dawaki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Za Mu Hada Kai Da Gwamnoni Domin Yakar Shaye-Shaye – Bala Dawaki

Published

on


Alhaji Bala  Saluhu Dawakin Kudu shi ne  Shugaban Kungiyar National Youth Chambers Council Of Nigeria, Kungiyar da ke rajin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, mai yawan fashin baki kan harkokin ci gaban matasa. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Bala Dawaki ya bayyana takaicinsa bisa yadda ake kara samun karuwar miyagun kwayoyi a kasar nan, sannan kuma ya jinjinawa mai martaba Sarkin Kano bisa tsayuwar daka da ya yi wajen ganin dole sai an gyara harkokin matasa tare da kawar da matsalar shaye-shaye. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

 

Da farko za mu so jin wanda muke tare da shi?

Sunana Bala Saluhu Dawakin Kudu  Kuma ni ne Shugaban

kungiyar National Youth Chambers Council Of Nigeria, Wannan kungiya ceda ke ya ki da muyagun  dabi’u kamar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yaki da jabun maganguna wanda ake shigo da su kasar nan wadanda ke lalatatarbiyar yaranmu.

Saboda haka babban aikin wannan kungiya bai wuce

kokarin tsaftace rayuwar matasan wannan kasa tare da wayar da kan matasan domin kaurace wa wannan mummunar dabi’a.

Tunda ayyukan wannan kungiya kamar yadda ka ambata shi ne yaki da shatare da wayar da kan matasa kan matsalar shaye-shaye, idan haka nemene dangantakar wannan kungiya da hukumar nan mai yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA)?

Ita wannan hukuma ce ta gwamnati wadda aka kafa domin gudanar da irin wannan aiki wadda gwamnati ke daukar nauyin al’amuranta, ita kuwa wannan ta mu kungiya ce mai zaman kanta wadda duk wanda ka gani sa kansa ya yi domin bayar da irin tasa gudummawar domin kawar da wannan bakar ta’ada. Sannan kuma ya kamata jama’a su sani dole sai jama’a sun

hada kai wajen  tallafawa gwamnati wajen yaki da wannan mummunar dabi’a wadda a halin yanzu ke neman zamewa al’ummar kasar nan kadangaren bakintulu. Hakan ba za ta samu ba har sai an hada kai da ire-iren wadanan kungiyoyi domin kamar yadda aka sani masu aikata wadancan laifuka a cikin al’umma suke ba aljanu ba ne balle a ce ba a ganinsu, kuma ‘ya’yan wane da wane ne duk an san su, saboda haka idan ana samun irin wannan kungiyoyi za a samu damar yakar matsalar cikin kankanen lokaci.

Tunda ka ce ita wannan kungiya ta hadin kan al’ummace shin ko wadanne matakai kuke bi domin ganin ayyukan kungiyar ya isa inda kuke fatan isar da sakon na ku?

Gaskiya ne kamar yadda aka sani ita wannan kungiya ta kasa baki daya ce wadda nake shugabanta, akwai musulmi, kirista kai har ma da wanda ba shi da addini, saboda haka hanyoyin da muke bi wajen isar da sakonnin wannan kungiya akwai harkar wayar da kai da kuma fadakarwa ta

hanyar amfani da kafafen yada labarai na Radiyo da Talabijin da Jaridu. Ko shakka babu idan ka dubi rayuwar matasan wannan lokaci na cikin hatsari wanda kuma an yi ittifakin cewa su ne manyan gobe, yanzu idan kana neman dan fashi da makami matashi ne, garkuwa da mutane matasa ne, shaye-shayen miyagun kwayoyi matasa ne da dai sauransu duk za ka tarar matasa ne.

Kuma idan ka bincika abubuwan da suka haifar da wadannan bala’an bai wuce amfani da tare shan miyagun kwayoyi ba, saboda haka wannan kungiya ta kuduri aniyar tsunduma cikin gagarumin aiki, kasancewar duk masu wannan dabi’u matasa ‘yan uwanmu ne kuma an ce  mai daki shi ya san wurin da ke masa yoyo.  Muna amfani da Sarkaunan gargajiya kasancewarsu iyayen kasa za su taimaka kwarai da gaske ganin cewa suke tare da

wadanann jama’a. Muna zuwa domin isar da sakonni kuma idan ka samu hadin kan wadannan rukunin sarakuna, kama daga mai unguwa ko dagaci, ko hakimi zuwa mai martaba Sarki suna bayar da gudummawa kwarai da gaske.

 Da ka ambaci sarakunan gargajiya sai ka tuna mana a kwanakin baya mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana aniyar fadarsa na cewar ba wanda za a kara nada wa wata sarautar karagajiya har sai an gwada kwakwalwarsa, shin ko mene ne hangen wannan kungiya kan jawabin Sarkin na Kano?

Wannan Jawabi abu ne wanda haka ya kamata duk masu rike da madafun iko kama daga sarakuna zuwa ‘yan siyasa kowa ya yi, mai martaba Sarkin Kano muna godiya da irin gudummawar da yake bai wa duk wata harka da ta shafi inganta rayuwar al’umma, musamman matasa

kasancewa shi ma cikin rukunin  yake na masu kananan shekaru, sannan kuma Allah ya yi masa baiwar ilimin addini da  na zamani ga kuma gogewa ta fuskar harkokin yau da kullum. Saboda haka wannan kungiya na tare da Sarki kuma muna jinjina wa kokarinsa. Saboda haka Sarkin Kano Uba ne na gari mai kishin al’ummarsa.

Ya dangantakar wannan kungiya take  tsakanin ta da gwamnonin kasar nan?

Wannan kungiya na da kyakkyawar alaka da gwamnonin Nijeriya, yanzu haka muna na shirye-shiryen  ganin an kaddamar da wannan kungiya a daukacin Jihohin Nijeirya.  Kuma muna kara godiya ga kungiyar matan gwamnonin Nijeriya, Kasancewarsu mata iyayen al’umma wanda idan ka samu ingantaciyyar uwa  kamar ka inganta al’umma baki daya ne, saboda haka wadannan matan gwamnonin Nijeirya suna bai wa wannan kungiya cikakken goyon baya yadda ya kamata.

Matsalar Shaye-shayen miyagun kwayoyi wasu na ganin kamar laifin gwamnatoci ne, musamman yadda idan ana kama manyan dilolin da ke safarar kwayoyin sai ka ga kwana daya zuwa biyu sun fito tare da ci gaba da gudanar da bakar sana’ar ta su, shin wai a ina gizo ke yin sakar ne?

Wannan tambaya ta zo a kan gaba kasancewar mun gudanar da taro a Abuja kwanan nan inda muka gabatar da shawarar neman yadda za mu zauna da ita hukumar da gwamnati ta dora wa alhakin yaki da shan miyagun kwayoyin, domin ganin an samar da mafita kan wannan matsala da ke addabar al’umma. A zaton wannan kungiya akwai inda gizo ke sakar,ko dai akwai daga cikin jami’an wannan hukuma da ke bayar da kariya ga masu waccan bakar ta’ada  ko kuma dai ana samun wata fahimta juna a tsakaninsu.

Babban tashin hankalin da ke damun jama’a shi ne idan aka samu labarin wani babban dila da ke gudanar da sana’ar sayar da kayan shaye-shaye kuma aka tsara zuwa kamo shi,sai ga wani daga cikin wadannan jami’an tsaro ne zai buga masu waya ya sanar da shi cewa lokaci kaza za a kawo samame wurin ka saboda haka ku kauce daga wurin.  Wannan na kara wa masu wannan sana’a karfi suna da wakilai daga cikin jami’an wadanda suke bai wa kudade. Ina tabbatar maka da cewa a gabana aka kira wani dila tare da shaida masa cewa ku bar wurin nan zamu shigo kame, saboda

suka ce kowa ya gudu amma fa sai sun hada wa wannan jami’i da ya sanar da su kudi.

Saboda haka, muke kira ga wannan hukuma da dinga gudanar a bitoci ga jami’anta domin fadakar da su illolin abin da ke cikin abubuwa da wasu bata-gari daga cikinsu ke aiwatarwa, domin su sani wannan aikin dasuka aiki ne na Allah, idan suka rungume shi da gaskiya sai Allah ya taimake su. Don haka wannan kungiya ke kokarin kai ziyara zuwa wannan hukuma domin bayyana masu irin abubuwan dake faruwa da jami’an su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai