Ana Ci Gaba Da Kiran Nasir Gawuna Ya Nemi Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Ana Ci Gaba Da Kiran Nasir Gawuna Ya Nemi Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya

Published

on


Ana ci gaba da kiraye-kiraye akan Kwamishinan ma’aikatar gona na jahar Kano, Alhaji Dokta Nasir Yusuf Gawuna ya fito dan neman takarar Sanatan Kano ta tsakiya.

Masu kiraye-kirayen suna ganin cancantar kwamishinan saboda irin rawarda yake takawa a siyasar jahar kuma mutumne daya soma siyasa tun daga tushe kuma bai taba barin al’ummarsa ba.

Cikin masu ganin cancantar Dokta Nasir Yusuf Gawuna harda wadanda ma ba yan jam’iyyarsa ta APC ba wani jigo dan siyasa a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Nasarawa daya nemi mu sakaya sunansa ya ce tabbas Nasir Gawuna dan siyasa ne me kyakkyawar mu’amala daya dace da wannan matsayi, wanda suma da suke ba’a jam’iyya daya dashi ba za su iya bashi goyon baya.

Yayi nuni da cewa Dokta Nasir Yusuf Gawuna Mutumne mai karamci da mutunta jama’a da kuma taimako ko lokacinda yayi shugabancin karamar hukumar Nasarawa karo uku ofishinsa ya zama na duk al’ummar jahar kano ne,haka wasu ke baro kananan hukumominsu suzo da bukatunsu wajensa saboda nanne ake sauraronsu dayi musu daidai gwargwado abinda ya sawwaka.

Ya ce wannan takara ta Sanatan Kano ta tsakiya da ake son Gawuna ya tsaya abune da bazai wahalar tallatuwa ba’a Kano ta tsakiyar domin mutumne na mutane,ko a wannan mataki na kwamishina da yake kai yana jajircewa akan al’amuran jama’a ci gaban jama’a shi yasa gida da ofishinsa yana tareda jama’a.

A nasa bangaren kwamishinan ma’aikatr Gonan na Kano Dokta Nasir Yusuf Gawuna wanda ake masa kiran takarar Sanatan ya shaidawa jaridar leadershipAyau a yayin zaben shugabannin jam’iyyar APC na Kano   cewa yaji wannan kira kuma a shirye yake  da wannan takara ta Sanata nan gaba kadan zai bayyanawa al’umma matsayinsa da tsare-tsare.

Dokta Nasir Gawuna ya godewa al’ummar Kano bisa wannan fata da suke masa tareda kiransu akan su ci gaba da baiwa Gwamnatin APC a jaha da kasa baki daya goyon baya dan sake maimaita mulkin Shugaba Buhari da Gwamna Ganduje a 2019.

 

Advertisement
Click to comment

labarai