An Bukaci Hausawan Legas Su Rungumi Akidar Zaman Lafiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Bukaci Hausawan Legas Su Rungumi Akidar Zaman Lafiya

Published

on


Anyi kira ga ‘yan Arewacin kasar nan mazauna jihar Legas da kewaye dasu tabbatar da sun rungumi akidar zama da makwabtansu lafiya duk da banbancen siyasa dake tsakaninsu, Sarkin Hausawan babbar kasuwar sayar da kayan gwarin jihar Legas Alhaji Haruna Jibrin dake unguwar mile12 a karamar hukumar Ikosi Isheri Ketu, ya bayyana haka a sakon barka da sallah ga al’umar yankin mile12 da jihar Legas baki daya a daidai lokacin da ake ci gaba da bukuwan sallah. Ya tattauna ne da manema labarai a jim kadan da kammala salla idin karamar sallah a filin idin unguwar Mile 12.
Sarkin Hausawan ya ci gaba nuna farin cikinsa ga al’ummar musulmi na kammala wannan azumi lafiya sannan ya yi kira ga jama’ar jihar Legas masamman ‘yan asalin Arewacin Nijeriya dake zaune a jihar Legas dasu ci gaba da biyayya ga shuwagabanin da kuma hakuri da zama da sauran kabilan jihar da sauran Al’umma domin samun karin zaman lafiya mai dorewa a duk fadin jihar.
Ya ci gaba da cewar, ko a wajen sallar idi da shida limamin masallacin idin kuma limamin masallacin jumma’a na ‘yan darika malam Liman Ba’are sun yi wa al’ummar mile12 irin wannan jawabi na bin shuwagabani da kuma bin doka da oda a jihar Legas.
Daga nan ya ci gaba da fatan alhari ga Hausawan jihar Legas domin ganin an kammala bikin wanna sallah lafiya. Sannan ya mika barka da sallah ga shugaban kasuwar Alhji Haruna muhammed Mai Dankalin Turawa dashi da sauran sarakunan Hausawa mazauna Legas.
A nasa jawabin, sakataren kungiyar limaman Mile 12 Malam Suleiman Ba’are, ya kara jira ne ga jama’a musulmi su kara kaimi wajen yi wa kasa addua’a da fatan alhairi, ya kuma bukaci masu hannu da shuni su ci gaba da taimaka wa marayu da sauran marasa galihu a cikin al’umma, ya ce, kungiyasu ta tallafa wa marayu fiye da 64 kanakin baya

Advertisement
Click to comment

labarai