Connect with us

ADABI

Yadda Taron Barka Da Sallah Na Kungiyar Tsintsiya Ya Gudana

Published

on

Taron dai na kungiyar Tsintsiya Writers Association Kano, da ta gudanar ta shirya shi ne misamman don taya yan uwa marubuta, da manazarta, da makaranta, da ma musulman duniya gaba daya murnar barka da sallah karama da kuma kammala ibadar azumin watan Ramadana. Wannan dai shi ne karo na Biyu da kungiyar ta shirya irin wannan taron na barka da sallah. Domin a shekarar da ta gabata ma ta 2017 ta shirya irin wannan taron kuma a irin wannan lokacin na bikin sallah karama.

Taron dai na bana da aka yi masa take da Allah Ya Maimaita Mana an yi shi ne ranar Litinin din da ta gabata wacce ta yi daidai da 18 ga Yuni, 2018 wato. An gabatar da taron ne a dakin taro na Gandun Albasa Primary da ke bayan Gidan Zoo, Kano.

An fara taron ne da misalin karfe 11:40 na safe. Marubuci kuma mawallafi Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) shi ne jagoran da ya jagoranci taron, inda ya fara da gabatar da manyan bakin da za su hau kan babban tebir. A farko ya fara kiran:

*Jamilu Haruna Jibeka, shugaban kungiyar marubuta Hausa ta Hausa Authors Forum.

*Ibrahim Hamisu, shugaban kungiyar marubuta wakoki ta kasa reshen jahar Kano.

*Hassana Abdullahi Hunkuyi, wakiliyar kungiyar marubuta mata zalla ta Mace Mutum Writers Association.

*Fatima Hussain El-Ladan. (Marubuciya mai abun mamaki)

*Abubakar Musa Abban Jiddah, shugaban kungiyar Aminci Writers Association Dambatta.

*Danladi Haruma, sakataren kudi na kungiyar ANA Kano, kuma mashawarci na musamman a kungiyar marubuta wakokin Hausa ta Najeriya.

*Eng. Bashir Isyaku Hotoro, shugaban makarantar bayar da horo a kan na’ura mai kwakwalwa ta Trobleshooting Information Technology, kuma memba na kungiyar ANA kano da kuma HAF,

*Al-Amin Daurawa, sakataren kungiyar marubuta ta HAWAN.

Bayan fito da manyan baki ne aka nemi Ustaz Muttaka A Hassan don ya bude taro da addu’a, kana dukkan mahalarta suka gabatar da junan su, sannan jawabin maraba ya biyo baya daga bakin jami’in yada labarai na kungiyar Zaid Ibrahim Barmo, inda ya yi wa dukkan baki barka da zuwa tare da neman afuwar jinkirin da aka samu na rashin fara taron a kan lokaci.

Bayan jawabin maraba, shugaban kungiyar ta Tsintsiya Writers Association, wato Zubairu M. Balannaji ya yi jawabi game da makasudin shirya wannan taro inda a ciki yake cewa:

“Burinmu a samu soyayya da shakuwa, da hadin kai a tsakanin marubuta da makaranta da kuma manazarta. Amma hakan fa ba zai samu da fatar baki kawai ba, kuma ba zai iyu wannan yana waccan duniyar, wancan yana wata nahiyar ba, don haka a hadu a waje guda a gaisa, a yi musayar ra’ayi a zahiri ba wai a yanar gizo ba, a yi raha kana a yi barkwanci, a selfa juna, wannan ko ba a fada ba an san zai karfafi zumunci da hadin kai, kuma zai kara mana kaunar juna.”

Shugaban ya kara da cewa: “Bayan haka son kara karfafa alaka tsakanin marubuta da makaranta, musamman ma saboda makarantan da ba su da hanyoyin ganin marubutan da suke gwanayensu. To wannan taron zai ba su damar ganinsu bil aini, har su yi zumumci wanda kowa ya sani shi zumunci alheri ne.”

Daga nan kuma gabatar da don karawa juna sani ta biyo baya, mukalar da Malam Lawan Muhammad Prp ya gabatar mai taken Rabe-Raben Salo A Kagaggen Labari ta yi gamsasshen bayani ne a kan salo da kuma rabe-rabensa. Bayan ya kammala ne ya amsa tambayoyi daga mahalarta.

Sannan ne kuma aka kira wasu marubuta da musamman aka gayyato su domin su amsa tambayoyi a kan littattafan da suka wallafa, su ne:

-Hassana Abdullahi Hunkuyi

-Nazeefa Sabo Nashe

-Abdullahi Jibrin (Uncle Larabi)

-Asma’u Lamido

-Fatima Hussain El-Ladan

Bayan fitowar su me kuma aka gayyato marubuci  Jamilu Haruna Jibeka tare da Zahraddeen Nasir a matsayin alkalan da za su tantance tambayoyin da za a yi, domin bayar da kyautuka ga wadanda suka yi tambayoyi mafi ma’ana. Marubutan kam sun sha ruwan tambayoyi tibis da marau, wadanda suka haifar da muhawara a tsakanin marubutan da makaranta.

Su ko alkalan da aka nada, sun fitar da jerin sunayen zakwakuran da suka fi yin tambaya mafi ma’ana da jan hankali, daga mataki na daya zuwa na Shidda. Su ne kamar haka:

1- Adam Tukur Miyetti

2- Danladi Haruna

3- Lawan Muhammad Prp

4- Zainab Hamza Adam

5- Mohd I. A Soke Lefe

6- Aminu Salisu Sodangi

Wadanda suka yi nasarar sun karbi kyautukansu daga hannun marubuci Jamilu Haruna Jibeka, kana aka ba manyan bakin da suka albarkaci taron damar fadin wani abu, inda a nan kungiyar ta Tsintsiya Writers Association ta sha yabo da jinjina saboda irin namijin kokarin da ta yi na hada zumunci a tsakanin marubuta. A cikin jawabinsa da ya yi Malam Danladi Haruna, ya bukaci marubuta da su zama masu zurfafa bincike sosai a kan abun da za su rubuta, su daina gaggawar fitar da littafi daga buhu sai tukunya, domin makarantan na yanzu ba irin na da ba ne da sai abun da kawai aka rubuta musu, saboda su na yanzu wasu sun ma fi wasu maeubutan bin diddigin abubuwa, domin kafofin sadarwa na zamani sun yawaita kuma damar yin amfani da su ma ya saukaka.

Shi ko Malam Jamilu Haruna Jibeka, kira ya yi ga marubuta da su dada tsarkake rubutunsu, ya zama mai ma’ana ta hakika kuma mai gamsarwa.

Sannan suna kallon sakon da za su isar a cikin rubutun ba wai abun da za su samu ba, domin kowanne marubuci za a tambaye shi game da abubuwan da ya rubuta.

A karshe Hajiya Kubra Abdullahi ta yi jawabin godiya tare da fatan alheri ga dukkan mahalarta sannan aka rufe taro da addu’a. Karfe 3:10 na yamma aka sallami kowa.

To fatan Allah ya karbi ibadarmu kuma ya maimaita ma na. Ameen.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!