Connect with us

ADABI

‘Wani Al’amari’ Na Rabi’atu Adamu Shitu

Published

on

A cikin filinmu na yau na Taba Ka Lashe da yake kawo muku gajeran labari daga fasihan marubuta, da kuma tsakure daga cikin littattafan magabata da ma na marubutanmu na yau da suke tasowa, ko kuma ma daga cikin rubuce-rubucen marubutan yanar gizo da su ma suke matukar bayar da gudummawa a adabin Malam Bahaushe a yau.
A cikin filin namu na ‘Taba Ka Lashe’ mun tsakuro muku labari ne daga littafin Wani Al’amari na fasihiyar matashiyar marubuciya Rabi’atu Adamu Shitu. Ita dai Rabi’a marubuciya da ta shigo duniyar rubutu da littafinta na Bakin Jinina, zuwa yau Rabi’a tana da littattafai har guda goma, daga cikinsu akwai Dan Kuka, Ni Ce Na Dace, Alkiblata, Wani Al’amari, Takaicina Farin Cikina, Ba Aljanna Ba Ce, Zanen Dutse da dai sauransu. Ga dai tsakuren labarin daga cikin littafin na WANI AL’AMARI a sha karatu lafiya.
Taron jama’a da suka yi dafifi a cikin gidan rawar dake Sabon Gari, har ya zama babu masaka tsinke a cikin gidan, alhazawa na zazzaune, a gabansu akwai lemuka na korawa, da yawansu kuma karan sigari ne a hannunsu suna zuka suna fesarwa sama, saman na cakudewa da kurar da matan da mazan da suke tikar rawa suna tayarwa, don haka kurar ta zama wani iri babu dadin shaka da gani idan har ba ka yi sabo da zama a irin wajen ba, ji za ka yi numfashinka yana neman daukewa, amma wani ikon Allah manyan mutane dattawa, suna zaune suna rawa sa kafada saboda yadda tashin kidan wakar ‘Bayan Rai’ ke tashi.
Daga cikin alhazawan akwai masu yunkurin a fusace su je tsakiyar gurin da suke masa lakabi da ‘plour’ su watsa wa uarinyarsu kudi su dawo mazauninsu su zauna.
Ahaji Na Malle na daya daga cikin alhazawan da suka zamk gatan gidan, don haka da yawan ‘yan matan da suke casa rawa ba suna yi ne don samun wani abu da sauran tarkacen mazajen da suke ta bulbula kudi ba, babban burin kowacce kilaki a gurin shi ne Alhaji Na Malle ya yi mata yayyafin kudi, domin nuna yabawarsa a gare ta.
Sai dai kash! Ga dukkan alamu Alhaji Na Malle ba shi da niyyar mikewa daga gurin, idan ka nutsu da kallonsa za ka ga alamar matsananciyar damuwa a tattare da shi, idan kuma ka matsa daf da shi, za ka fahimci cewa damuwar ce tsantsa a kan fuskarsa. Don haka wadanda suka kusance shi suka daina damun kansu da sai sun cusa kansu a inda yake, musamman manyan abokansa ‘yan kasuwar da suka dauke zuwa ‘Primier’ kamar wajibi ce a gare su.
Wayarsa ce ta yi kuka, don haka sai ya dauki wayar ya kara a kunnensa, amsa daya biyu ya bayar sannan ya kashe wayar ya ci gaba da tagumi yana kallon tsakiyar gurin da ake yin rawar.
Wata matashiyar Bafulatanar yarinya da ake mata lakabi da Aina Mishan. Ta tsaya da rawar da take yu ta dubi screen din kan wayarta ta saka a kunnenta sannan ta yi saurin ficewa daga cikin taron don ta samu jin abin da ake sanar da ita.
“Buhari ne, kina ina?”
“Ina nan Primier, ba ka san yau ake Birthday din Aysha Super ba”
“Na sani, ba zan zo wajen ba ne, kin san ina da matsala da Suwaiba
Ashiwariya, na tabbata dukan da na yi mata jiya ba za ta hakura ba sai ta san yadda ta yi ta nemo kwalawa, yanzu ya za a yi mu hadu, ina nan wajen gidan mangoro.”
“Me kuma zan yi maka, ni fa ban son takura Baharu.”
“Ba takura miki zan yi ba, ina son na tsirar da ke ne, kin san dai halina bana cikin wadanda suke son cutar da ke.”
Ta yi shiru tana tunani daga can kuma sai ta ce: “Ka fuskanci wani abu ne, don yau na ga ran mutumin kamar a bace yake ko maganar kirki ba ya yi, ya daure fuska kamar wanda aka cusa masa bakin cikin duniya.”
Baharu ya yi dariya, daga bisani ya ce: “Ki yi maza ina tsoron miki tarkonsa, yau ya saka dambar ko ta halin kaka sai ya cimma burinsa a kanki, idan ba haka ba kuma zai iya kashe ki, na samu labarin ne daga wajen Bala Balbo abokina, saboda su ya ba wa kwangilar aikin.”
Ta rike baki a tsorace ta ce: “Da gaske ko da wasa Baharu?”
“Ba da irin wadannan zantukan ake wasa ba Aina, kuma ba ni ne ya kamata ba yi miki irin wannan wasan ba, Allah da gaske nake yu.” Ta shiga tashin hankali a cikin kankanin lokaci ta fara rikrkicewa.
Kafin ta bar inda take wayar ta ji sautin tafiya a bayanta, don haka a tsorace ta waiga, amma sai ba ta ga kowa ba, ta yi maza ta shige cikin gidan, babu amana a bariki don haka ba za ta sanarwa da kowa halin da take ciki ba.
Ta shiga filin ta hango babu Alhaji Na Malle a mazauninsa, don haka sai rudu ya kara shigarta ta kara rikirkicewa. Ta yi saurin tattara abubuwan da ya rage mata a gun ta nufi hanyar waje da sauri.
Ji ta yi an dafa mata kafada ta baya, a tsorace ta juya cikin firgici, nan ta ga ashe kawarta ce Ashanti Swarga.
“Har kin ba ni tsoro.”
Ashanti ta tuntsure da dariya “Na gan ki ne a tsorace, wani abu ne ya faru ko kin ji labarin ‘yan sanda za su zo kama mutumin naki?”
Ta yi saurin girgiza kai “Ba ni da wannan labarin, wata samuwa ce, idan na dawo kya ji labari.”
“Aina ke fa shegiyar yarinya ce Wallahi sai ki dinga raina wa mutane hankali, samuwar ta zo irin wannan da za ta kidima ki amma ki kasa sanar da ni, ni ma na rude kamar yadda kika yi din nan, wanne otal ne?”
Bakinta na sarkewa ta sanar da ita cikin saurin baki: “A mota ake jira na ban san inda muka nufa ba.”
Ashanti ta tuntsure da dariya ta yi gaba tana ci gaba da sangartacciyar maganarta irin nasu na ‘yan bariki gogaggu.
Aina ta yi maza ta rataya jakarta da ta zamlo, ta fice da sauri-sauri gudu-gudu. Ta tsaya a bakin hanya tana jiran abun hawa, a lokacin dare ya yi don misali ne na sha daya da mintuna, idan kana cikin gidan ba za ka yi ysammanin tara ta yi ba ma, amma da ka fito za ka ga alamar dare domin yawancin masu sana’ar kan hanya sun watse, saboda yanayi na sanyi da ake yi.
Tsayuwar jiran A-daidaita-sahu take, amma babu ko kyallin abin hawa, hakan ya sa ta fara raba tunaninta kashi Biyu, ko dai ta koma cikin gidan idan an tashi ta bi abokan tafiyarta su tafi tare, sai kuma ta girgiza ganin yiwuwar hakan da wahala saboda kowa zai iya kasancewa ta samu saurayin da za su fice da shi, kuma a kan ta bisu su rage mata hanya sai ya zama abun rigima a wannan zaman nasu da kowa ya ke dardar da wata ta kusanci saurayinta. To ya za ta yi?

Za mu cigaba in sha Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!