CBN Zai Kara Yawan Bashin Da Yake Ba Mata ‘Yan Kasuwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

CBN Zai Kara Yawan Bashin Da Yake Ba Mata ‘Yan Kasuwa

Published

on


Babban bankin kasa CBN, ya sanar da cewar yana yin hadaka da cibiyar inganta ruyuwar mata NCWD ta kasa don kara samar masu da bashi don inganta sana’o’in su.

Shugaban sashen tsare-tsare na bankin Attah Joseph ne ya bayanna hakan a lokacin da ya kai ziyara a shalkwatar kungiyar dake Abuja, inda ya kara da cewar, akwai bukatar a kara samarwa da mata damar samun kudi kuma anyi ganawar ce don a samar da shirye-shirye din magance kalubaken da mata suje fuskanta a kadar nan.

Ya yi nuni da cewar, kudi suna da mahimmanci gaske wajen habaka kasywanci kuna an gano cewar yadda mata suke samun sykunin kaiwa ga kudi ana nuna banbanci duk da mahimmancin da suke dashi wajen gina kasa.

Acewar sa, a bisa binciken da muka gudanar a 2017, an gano cewar kashi 42.3 bisa dari na maza suna da asusun ajiyar banki, inda mata kuwa suke da kashi 30 bisa dari kacal kuma kasashen da keda asusun ajiya a bankuna sunfi samun ci gaba wajen inganta rayuwar alumar su.

Da take mayar da nata jawabin, Darakta Janar ta kungiyar Mary Ekpere-Eta ta ce, cibiyar tana kawai samun dauki ne daga gwamnatin tarayya kuma kudib basa isar ta aiwatar da ayyukan ta, inda ta bukaci bankin da ya tallafawa kungiyar don ta samu damar aiwatar da ayyukan ta a kada baki daya.

Acewar ta, a kwanan baya mun horas da mata akan wasu sanaoin hannu muka kuma basu kudi don su fara sana a, sai dai muna fama da karancib kudi.

Ekpere-Eta ta kara da cewar akwai rawar da kungiyar zata iya badawa wajen ganin gwamnatin tarraya ta cimma kudurorin data sanya a gaba, musamman wajen habaka matsakaitun sanao I, ta kyma roki bankin da ya taimaka wajen samar da mata kudi don habaka sanao in su.

A karshe  Ekpere-Eta ta ce, bayanan da cibiyar ta tara  bankin zai uya yin amfani dashi a matsayin madogara don baiwa cibiyar tallafi yadda mata masu sanaoi za a inganta sanaoun su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!