Shirin Kora Bai Shafi ‘Yan Kasuwan Nijeriya Dake Ghana Ba –Ambasada — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Shirin Kora Bai Shafi ‘Yan Kasuwan Nijeriya Dake Ghana Ba –Ambasada

Published

on


Ministar harkokin basashen waje da hada yankuna na basar Ghana Shirley Ayorkor-Botchwey, ta sanar da cewar yan kasuwa yan Najeriya dake cikin basar korar da gwamnatin basar ta yi a Keenan baya bata shafesu ba.

Botchwey ta bayyana hakan ne a lokacin data kaiwa takwaranta Ministan harkokin basashen waje na Najeriya ziyara Geoffrey Onyeama a Abuja a ranar Litinin data gabata don tattaunawa akan harkar kasuwanci a tskanin basashen biyu.

In za a iya tunawa bungiyar yan kasuwa ta Najeriya dake Ghana ta yi barazanar cewar korar da za a yi zata iya janyo mummunar zanga- zangar nuna byama a basar ta Ghana.

Har ila yau, Botchwey ta nanata cewar, yan kasuwa yan Najeriya da kuma basashen dake cikin bungiyar ECOWAS korar bata shafesu ba.

Acewar ta, gwamnatin mu tana yin dukkan mai yuwa don ganin ta tattauna da bungiyar ta yan kasuwa da kuma sauran yan kasuwa dake cikin bungiyar  ECOWAS

Da yake mayar da nashi martanin Onyeama yace, zuwan Ministar Najeriya ya nuna a zahari Ghana ta damu da yan kasuwa yan Najeriya dake Ghana.

Onyeama yaci gaba da cewa, gwamnatin Ghana bata ji dadi ba akan lamarin saboda suna son subi ba’idar yarjejeniya ta kasuwanci da fitar da kaya ba tare da wata tsangwama ba a bisa sharuddan da ECOWAS ta shinfida.

A barshe yace, ya kamata Ghana ta yi la’akari da dogon danbon zumuncin dake tsakanin ta da Najeriya kada korar ta jefa rayuwar yan Najeriya dake Ghana a cikin matsala.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!