Connect with us

TATTAUNAWA

Sirrin Yadda Na Ke Tafiyar Da Al’amurana –Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Za a iya MALAM IBRAHIM KHALIL mashahurin malamin addinin Islama a jihar Kano, Najeriya da ma yankin Afrika, wanda ya tsunduma a cikin harkokin siyasa; lamarin da ba a saba gani ba a kasar Hausa. To, amma duk da kasancewar sa shugaban majalisar malamai ta kasa reshen jihar Kano da ma irin surutan da a ka yi, hakan bai hana shi cigaba da gudanar da harkokin siyasarsa ba. EDITAN LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu damar yin babban kamu, inda ya yi wata doguwar tattaunawa da shehin malamin kan harkokin siyasa da kuma salon yadda ya ke bayar da fatawa. Za mu rika tsakuro mu ku tattaunawar a duk mako har zuwa karshenta. Sheikh Khalil, wanda bai cika son bayar da tarihin rayuwarsa ba, Nasir Gwangwazo ya fara ne da inda ya nemi ya gabatar da kansa. Bisimillah:

 

Akaramakallahu, za mu so ka fara da gabatar da kanka bisa tsarin da ka ke so.

Bisimillahir rahamanir rahim, alhamdulillahi rabbir alamin, wassalatu wassalu ala asharatul mursalin, assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu. Ni sunana Ibrahim Khalil Kano. Ni mutumin Kano ne dan kasuwa manomi, wanda ya ke karantarwa a al’amura na addini, mai kuma yin harkoki na siyasa, sannan wanda na ke shugabantar Majalisar Malamai ta Kasa Reshen Jihar Kano, sannan kuma na ke rike da ofishin mai ba wa gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, shawara a kan al’amura na musamman.

 

To, Akaramakallah, ga yanayin yadda ka gabatar da kanka mutane za su iya yin mamakin ka. Ka ce kai manomi ne, dan siyasa, mai karantarwa kuma dan kasuwa. Shin ya ka ke iya tafiyar da wadannan abubuwa haka?

Ai abubuwa sauki ne da su. ita rayuwa abubuwa biyu ta ke bukata. Na farko ka tsara jaddawali; abinda a ke cewa ‘time-table’. Shi kuma jaddawali ba za ka yi ba sai ka yi tsari; me ka ke yi? Me za ka yi? Me ka ke so? Ya za ka yi? Yaushe za ka yi? A ina za ka yi? Wato kamar yadda ku ’yan jarida ku ke cewa, ‘3W and H’. Cewa ‘What to do? Where to do? When to do? How to do?’ Shikenan, idan ka dauki wadannan manyan abokai da malaman falsafa fiye da shekara 1,000 su ka ce su ne manyan abokanka, to idan ka rike su a matsayin abokanka, ka dauke su a matsayin su ne ‘planning’, su ne tsari, to sai kuma ka zo ka yi jaddawali. To, idan ka tsara wannan, komai na duniya sai ka yi shi. Idan ka ga abubuwa su na tafiya ba a tsare ba, rashin tsarin ne da rashin ‘time-table’. Shi ya sa da ma abubuwa guda biyu su ne rayuwa; ‘time management’ da ‘planning’. Lokaci da tsari. Wadannan su ne su ke yin komai. Shi ya sa idan ka kalli rana Ubangiji ya yi ma ta wani tsari, wanda ya ke ba za ta canja ba har abada, sannan kuma ya dora duniya a kan wannan tsari na rana, sannan ya dauko wata ya yi ma sa wani tsari, sai ya gina wani tsari daban. Don haka shi ya sa har abada ba za ka samu canji ba. Don me? Saboda tsarin da a ka yiwa rana shi ne tsarin da ya kamata ka tafi a kansa, tsarin da a ka yiwa wata shi ne tsarin ya kamata ka gina wasu abubuwa. Amma mafi yawa abubuwan da a ka gina wata kansa, an gina su ne a kan rana. To, da rana za ka yi amfani. Duk lokacin da ka yi amfani da rana, za ka samu komai ya na tafiya daidai wa daida ba zai cude ba, domin kuwa rana  Allah bai dora ta a hannun wani ba. To, haka kai ma rayuwarka, da a ke cewa mutum tara ya ke bai cika goma ba, idan har ka iya tsara wadannan abubuwa guda tara, ka same su sosai, to wancan na goman ka yi maganinsa.

 

Masu karatunmu, wannan sharar fage ce kawai. Za mu dora makon gobe da yardar Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: