Ina Son Liberiya Ta Zama Kamar Super Eagles -Weah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Ina Son Liberiya Ta Zama Kamar Super Eagles -Weah

Published

on


Shugaban kasar Liberia kuma tsohon gwarzon dan kwallon duniya George Weah ya ce, Najeriya ta samu ci gaba sosai a fagen kwallon kafa kuma yana bukatar kasarsa ta yi koyi da tawagar Super Eagles.

Shugaban ya ce, a lokacin da yake matashin dankkwallo, ‘yan wasan Najeriya irinsu Stephen Keshi da Rashidi Yekini da Fridya Ekpo da sauransu na burge shi matuka kuma yanajin dadin yin kwallo dasu.

Wannan na zuwa ne bayan Weah ya nuna tsoffin dabarunsa a wasan sada zumunta da Najeriya da doke Liberia da kwallaye 2-1 a birnin Monrobia, in da ya buga wasan har tsawon minti 79 kafin a sauya shi ana saura minti 12 a tashi wasan.

A shekarar 1995 ne aka zabi George Weah a matsayin gwarzon dan wasan duniya da nahiyar Turai da kuma Afrika kuma har yanzu ba’a sake samun dan Africa ya lashe irin wadannan kyaututtuka ba.

Tsohon dan wasan wanda ya lashe kujerar shugabancin kasa da gagarumin rinjaye a zaben bara, ya kasance mutun daya tilo daga nahiyar Afrika da ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya kuma a cewarsa yana fatan nan gaba za a sake samun dan wasan Afrika da zai lashe kyautar ta gwarzon dan wasa a duniya.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!