Connect with us

MANYAN LABARAI

Boko Haram Ta Aika Wa Da Kauyukan Borno Uku Wa’adi

Published

on

Kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram su ba mazauna garin Jakana da Mainok na jihar Borno wa’adi na barin garin ko kuma su kawo musu hari.
Wata majiya daga garin Jakana ta bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan ta’adda sun ba mazauna garin zuwa jiya Laraba da su fice daga garin ko su fattatake su
“Bayan harin da suka kai garin Aunu, ’yan ta’addan sun bayar da sakon cewa mutane garin su gaggauta barin garin zuwa ranar Llaraba ko a kawo musu hari,” inji wani mazaunin garin.
Amma bayani daga garin ya nuna cewa, jami’an tsaro na sojoji tare da hadin gwiwar dakaru na musamman na gudanar da bincike a gidajen garin duk da kuwa hankalin jama’a sai kara tashi yake yi a garuruwan biyu dake a karamar hukumar Kaga na jihar Borno.
Binciken gida gida dake ne ake yi, an fara ne da sanyin safiyar ranar Laraba ana kuma ci gaba da aiwatar da shi har zuwa karfe sha biyu na rana, a garuruwan biyu dake a kan babar hanyar da ta taso daga garin Maiduguri zuwa Damaturu.
Majiya daga bangaren jami’an tsaro ya bayyana cewa, an dakatar da daruruwar motoci dake bin hanyar a yayin da sojoji suka kulle hanyar gaba daya.
“Muna aiki ne daidai da bayanai da muka samu, muna kuma gudanar da ayyukanmu ne don kare rayuwar jama’a da zaran mun kammala aikinmu zamu bude hanyar tare da daga takurawar da muka yi wa zirga zirgan motocin,” inji majiyar bangaren tsaro.
Matafiya da kamarin ya rutsa da su a tashoshin mota a bangaren da lamarin ya faru sun yi korafin rahin sanin halin a ake ciki, sun kuma nuna mamakin yadda za a rufe hanyar duk da an dage dokar hana fita da aka kakaba na karfe 6 na safe.
Da aka tuntubi shugabannin kungiyar masu sifirin motoci na NURTW na jihar Yobe, wani jami’i da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabatar da cewa, babu motar da ta bi hanyoyin da lamarin ya shafa a yau.
“Mun tuntubi rundunar sojoji don sanin dalilin rufe hanyoyin, amma suka bayyana cewa, ana wani aiki ne na soja a tsakanin garin Damaturu zuwa Maiduguri amma za a kammala ba da jimawa ba.
Haka kima a wata samara da aka bayar ranar Laraba da rana, sojojin sun bayyana cewa, suna gunadar da wani aiki na musamman ne don kakkabe wadanda ake zargin ‘yan ta’adda Boko Haram ne a kan hanyar.
“An jawo hankalin mu kan cewa wai sojoji sun rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lallai wannan ba gaskiya bane.
“Abin dake faruwa shi ne ana wani aiki ne na kakkabe yankin don korar wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne a kan hanyar Maduguri zuwa Damaturu.
“Wannan aikin na gudana ne don tabbatar da lafiyar mutane masu bin hanyoyin ne kuma da zaran an kammala za a bude hanyar nan take ga masu amfani da hanyar,” kamar yadda sanarwa mataimakin Daraktar watsa labarai na Operation Lafiya Dole’ Kwanel Onyema Nwachukwu, ya bayyana.
Rundunar sojojin sun shawarci jama’a su ba dakarun sojoji hadin kai a yayin da suke gabatar da aikinsu. Sojoji Sun Musanta Zargin Ruga Hanyar Maiduguri Zuwa Damaturu
Sojoji sun karyata kilace hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
A sanarwa da aka raba ranar Laraba da rana, wadda mataimakin daraktar watsa labarai na Operation Lafiya Dole’ Kwanel Onyema Nwachukwu ya asanya wa hannu, ya kara jadda cewa, sojoji na aikin kakkabe yan ta’adda Boko Haram ne a kan hanyar.
“An janyo hankalin mu a kan rade radin da ake yin a cewa, sojoji sun killace hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lallai wannan ba gaskiya bane,” inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!