Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu A Katsina

Published

on

‘Yan ta’adda da ba a san ko su wanene bane sun kashe mutum hudu a kauyen ‘Yar Santa dake karamar humumar Kankara ta jihar Katsina.
Bayani ya nuna cewa, tuni aka yi jana’izar mutanen da aka kashe kamar tadda addinin musulunci ya tanada a jiya Laraba.
Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwa lamarin ya kuma ce ya zuwa lokacin hada wannna rahoton ba shi da cikakken bayanain yadda kamari ya auku.
Majiyar mu ta bayyana mana cewa, ‘yan ta’adda sun kai hari a kauyen ne da misalin karfe 6 na yamma ranar Talata a dai dai lokacin da yawancin mutane garin suke da wowa daga babbar kasuwa garin Kankara.
An kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun shiga ne a kan babura kuma nan take suka shiga harbe harbe a kauye abin da ya sa jama’ar kauyen suka shiga guje-guje bangarorin daban-daban. Mutum hudu da suka mutu, harbin bindiga ne daga ‘yan ta’adda ya yi sanadiyyar mutuwarsu nan take.
‘Yan ta’adda sun kuma dawo ranar Laraba a dai dai lokacin da ake yin jana’izar wadanda suka rasun, in da nan take ‘yan sintiri da ke garin suka fattatake su.
Daya daga cikin mutane garin ya kuma ce, “Da safiyar yau a daidai lokacin da muke jana’izar wadanda suka mutu ‘ya ta’adda sun sake dawowa sai da ‘yan sintirin garimu suka fattatake su.”
Jami’in watsa labarai na ‘yan sanda ya kuma ce, tuni a ka tura jami’an tsaro kauyen don bayar da kariya.
SP Isah ya ce, “Lallai lamarin ya faru amma a halin yanzu mutanen mu na nan don shawo kan lamarin.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!