Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC Jama’ar Jihar Gwambe Za Su Zaba –Ministan Muhalli

Published

on

Ministan Muhalli, Alhaji Sulaiman Hassan, a jiya Alhamis ya bayyana cewa; yana da imanin cewa; al’ummar jihar Gombe, jam’iyyar APC za su zaba kwata a zaben 2019 da yake kara gabato mu.

Hassan ya tabbatar da wannan ne a garin Kaltungo dake karamar hukumar Kaltungo a jihar Gomben, a lokacin kamfen din jam’iyyar APC din jihar. Ya ci gaba da cewa; shi ya san a jihar Gombe, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da dukkanin ‘yan takarar dake jam’iyyar a jihar, su al’ummar Gombe za su zaba a zaben da za a yi. Ya ce; wannan taron jama’ar da suka taru a lokacin Kamfe din, ya nuna cewa; tabbas jam’iyyar APC za su yi nasara a zaben.

A nashi bayanin, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha,  ya ce; jam’iyyar APC jam’iyya ce ta ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Shima dan takarar Gwamnan jihar a jam’iyyar APC, Alhaji Inuwa Yahaya, ya ce; al’ummar Gombe, musamman kudancin Gombe inda jam’iyyar PDP ta fi karfi sun sha bakar wuya a hannun gwamnatin PDP din, ya ce; wannan dalilin yasa su fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna APC baya.

Rahotanni sun bayyana cewa; Gwamna  Jibrilla Bindow na Adamawa da Gwamna Mohammad Abubakar na Bauchi suna cikin wadanda suka halarci taron.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!