Connect with us

LABARAI

Shugaban Sarakunan Nasarawa Ya Kwanta Dama, Yana Da Shekara 84

Published

on

Allah ya yi wa shugaban Majalisar Sarakunan jihar Nasarawa Alhaji Isah Mustapha Awgai rasuwa, ya rasu yana da sheakara 84.
Da yake tabbatar da rasuwar ta sa a jiya Alhamis a lafiya, daya daga cikin ‘yan majalisar Sarkin, Ajiyan, Lafiya, Alhaji Sule Abubakar,ya ce marigayin ya rasu ne a Asibitin koyarwa na Nazemiya da ke Abuja a safiyar jiya Alhamis, bayan rashin lafiyar da ya yi.
Ya ce an haifi marigayin ranar 14 ga watan Maris na shekara 1934, kuma an nada shi a matsayin sarki a shekara ta 1974.
Marigayin ya yi karatun kur’ani a Kofar Kaura Lafiya yana cikin wannan sai aka sa shi a makarantar Elementare da ke Lafiyan a sheakara 1943.
Bayan ya samu kamala karatunsa a elementaren a shekara ta 1951, daga nan sai ya samu nasarar shigao Benue Probincial Middle School da ke Katsina-Ala.
Kammala wannan sakarandiren da ya yi cikin nasara a shekara ta 1958, sai ya wuce zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Sashin koyon mulki a shekara ta 1958 in day a samu Dufuloma a fannin Accountancy a shekara ta 1959,
Sannan ya kara da cewa, marigayin ya auri mata uku yana da ‘ya’ya biyu da kuma jikoki da dama.Kamar yadda ya ce marigayin ya yi bikin murnar haihuwarsa a ranar 4, Mayu,na shekara ta 2017, ya kuma shafe shekara 44 a gadon sarauta, kafin Allah ya yi masa rasuwa.
Marigayin ya yi kamar wata hudu yana fama da rashin lafiyar daga nan aka dauke shi zuwa kasar waje domin nema masa lafiya, daga baya kuma aka dawo da shi gida, sannan aka dauke shi zuwa wani asibiti da ke Abuja inda Allah ya yi masa rasuwa.Marigayi Isa Mustapha Agwai ya rike mukamai da yawa a aikin gwamnati
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!