Connect with us

LABARAI

Zargin Ministan Sufuri: Amechi Bai Zagi Buhari ba, In Ji Farfesa Wole Soyinka

Published

on

Babban marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka ya ce, ya karanta rahotanni da dama a kan wani jawabi na Minista Amechi da ke yawo a kafafen sadarwa, inda ake cewa Ministan ya zagi Shugaban Kasa Buhari, amma ya ce, shi bai ji inda ya zagi Buhari ba kamar yanda ake yayatawa.
Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taro kan labaran karya da BBC ta shirya a Abuja.
Da yake jawabi a wurin taron da aka yiwa take da ‘Nijeriya 2019: Yaki Da Labaran Karya’, ya shawarci ‘yan jarida da tantance labari kafin yadawa, sabanin yanda ake yi a kafafen sadarwa na zamani.
“Kwanaki biyu zuwa uku da suka gabata, na ci karo da wasu labarai a kafafen sadarwa na zamani, inda ake cewa Minista Amechi ya zagi Buhari, bayan da na saurari Jawabin, ban ji zagin da ake cewa ya yi ba, nace to kila akwai bukatar na sake koyon harshen turanci ne.
“Wani lokaci, ‘yan jarida suna jin kamar ba zasu iya gogayya da kafafen yada labarai ba, wannan bai kamata ya zama haka ba. Ku yi alfahari da aikin ku, kuna da girma da kima a cikin al’umma fiye da sauran kafofin sadarwa na zamani.
Minista Amechi shi ne shugaban Kwamitin kanfen na Buhari. A cikin wannan Jawabin, an jiyo Amechin yana cewa; Buhari baya karatu, kuma baya sauraren kowa.
“Shugaban Kasa baya sauraren kowa. Kana iya rubuta komai kaga dama, amma shi sam ko a jikinsa, to yana ma karatu ne?,” a cikin Jawabin na Amechi
A wani bangaren Jawabin kuma, Ministan ya gargadi yan jarida da cewar; ba zai sake gayyatar su ba idan har suka fitar da abun da yake cewa,” Wannan ba abun da zaku fitar bane a kafafen sadarwa ba. Idan har kuka sake kuka buga wannan labarin, to ba zan sake gayyatarku ba,” in ji Amechi a cikin ‘audion’.
“Shekaru uku na mulkin Buhari kowa kuka yake..’yan jarida kuka, yan siyasa kuka, Dalibai kuka, maoma kuka, shekaru uku kadai. Talauci ya karu, mutane na fama da yunwa, Nijeriya zata rabu,”
Ya ci gaba da cewa, “Ba randa kasar nan zata gyaru, na rantse. Idan har kasar nan zata gyaru, sai in za’a kashe kowa da kowa ne.
“Ba wani ci gaba da kasar nan take samu. Lokacin da Magnus yake Sakataren Gwamnatin jihar Ribas, na taba fada masa cewa, kasar nan ba wani fata a kanta, sai yace “Oga ka daian fadar wannan, bai kamata ace Gwamana ne ke fadar wannan ba.”
“Amman bayan wata biyu a Abuja, sai ya same ni yake fadaman cewa: ya yarda da abun da na fada, ba wani fata a kasar nan. Abun da kawai suke yi a nan Abuja shi ne rabon kudi.
Ministan Labarai, Lai Muhammad ya ce, wannan jawabin na Amechi ba zai shafi yakin neman zaben da jam’iyar APC take ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!