Connect with us

SIYASA

Sanata Ekwunife Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Atiku

Published

on

Sanata Uche Ekwunife, ‘yar takarar Sanatan Anambra ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP ta shawarci al’ummar jihar Anambra da su zabi jam’iyyarsu ta PDP a zaben cikin watan Fabarairu da zai gudana a shekararnan.

Ekwunife ta yi wannan kiran ne a lokacin wani gangami da wata kungiya mai suna ‘Peter Obi Good Governance Vanguard’ wato POGGV, ta shirya a garin Agulu dake Anaocha a yau Lahadi.

Ekwunife, wacce ta wakilci Obi a gangamin, ta bayyana cewa; ya kamata mutanen Anambra ba kawai Atiku/Obi za su za ba, su tabbata sun zabi dukkanin ‘yan takarar PDP a zaben 2019 da za a yi, wanda ya hada da ‘yan majaliusn jiha da na tarayya.

Ta ci gaba da cewa; Peter Obi a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP dan kasa na gari ne, inda ta bukaci da su zabe su a zaben da za a yi.

Ekwunife ta ce; ta bar jam’iyyar APC zuwa PDP ne a lokacin da aka zabi Obi a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, ta ce; saboda ba za ta iya Kamfen da nufin a ka da shi ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!