Connect with us

SIYASA

Yanzu Ne Ma Nijeriya Ta Ke Da Bukatar PDP –Kodinetan Kamfen Din PDP

Published

on

Cif Okechukwu Enekwe, daya daga cikin jigon jam’iyyar PDP a jihar Anambra ya yi kira al’ummar jihar da su zabi ‘yan takarar jam’iyyarsu a zaben da za a yi a watan Fabarairun shekararnan.

Enekwe, wanda yake shi ne Kodinetan Kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP na karamar hukumar Arewancin Orumba dake jihar, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Ajali dake Orumba din a yau Litinin.

Ya ce; jam’iyyarsu ta tsaidawa ‘yan Nijeriya da jihar Anambra ‘yan takarar da suka dace, tun kama daga kan ‘yan takarar shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya da na jiha.

Ya ci gaba da cewa; Atiku/Obi a matsayin ‘yan takarar shugabancin kasarnan a jam’iyyarsu shi ne abin da Nijeriya ke bukata domin farfado da tattalin arzikin kasarnan zuwa tudun mun tsira tare kuma da magance matsalar talauci da ya addabi ‘yan Nijeriya. Ya ce; “Muna kira ga mutanen Anambra, Kananan hukumomin Orumba ta Kudu da ta Arewa, da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi ‘yan takarar jam’iyyar PDP.”

Ya kara da cewa;  “Atiku Abubarkar da Peter Obi a matsayin ‘yan takararmu na shugabancin kasa da mataimaki, shi ne zabi mafi cancanta ga Nijeriya domin farfado tare da bunkasa tattalin arzikinmu da ya ri ga ya durkushewa. ‘Yan Siyasa ne da aka gwada su, kuma dukkanninsu masu fasaha a bangaren ‘yan kasuwanci ne.”

“Burinmu shi ne manoma, ‘yan kasuwa, ma’aikata, da dukkanin al’ummar mazabar Orumba da jihar Anambra baki daya su zabi jam’iyyarmu ta PDP, jam’iyyar da ta yiwa ‘yan Nijeriya ayyukan alheran da ba wata jam’iyya da ta yi musu.” Ya jaddada.

Enekwe har wala yau ya bukaci a zabi ‘yan takarar Sanatocinsu masu wakiltar Orumba ta Arewa da ta Kudu wanda ya hada da Chris Uba da kuma Misis Chinelo Nwankwo. Ya ce; ya kamata ko don nuna shaharar Obi a yankin su zabi jam’iyyar ta PDP.

Kodinetan Kamfen din, ya ce; Uba, wanda shi ne dan takarar Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, dan siyasa ne fitacce wanda yake da fasahar wakiltar mutane da kuma kawo ayyukan ci gaba da al’ummarsa.

Sannan ya yi kira ga masu zabe da su tabbata sun zabi ‘yan takararsu a lokacin zabe da za a yi, inda kuma ya shawarci wadanda ba su karbi katunan zabensu ba da su je su karba a makon nan. Ya ce; tunda INEC sun kara wa’adin karbar katin zaben, ya kamata mutane su yi amfani da wannan damar wajen karba na su domin kwace ragamar mulki zuwa ga wanda suke so.

Ya ce; ta janibinsu za su ga sun taimakawa mutane wajen ganin sun karbi katin zaben  su domin su zabi dan takararsu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!