Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutum Bakwai Sun Mutu Sanadiyar Gobarar Tanka A Anambra

Published

on

Ranar Lahadin data gabata mutane bakwai ne aka tabbatar da sun mutual sanadiyar gobarar motar Tanka, wannan al’amari dai ya faru ne kusa da msaukin gwamnan wanda yake a Amawbia kusa da hedikwatar babban birinin jihar na near Awka.
Wata majiya ta nuna cewar Gwamna Willie Obiano yana cikin gidan lokacin da al’amarin ya auku.
Wurin da jami’an tsaro suke na gidan Gwaman gobarar ta shafe shi, mutane da yawa ne dai asuka samu raunuka, a sanadiyar ita gobarar, wadda ta fara misalin karfe tara saura minti ashirin na dare ranar Adsabar, akwai kuma motoci da yawa, gidaje da kuma shaguna wadanda suka kone
Wanda ya ga abin da idanun shi ya bayyana cewar ita Tankar tayi kokari ne na bin wata lankwasa a wani shatale tale, lokacin data fadai ta kama da wuta.
Wanda abin ya faru a idon shi ya kara bayanin cewar, “ Wadanda ke kusa da wurin yawancin su ‘yankasuwa ne kanana, sun fara yin guje -guje saboda su ceci rayuwarsu, amma wsu daga cikin su wuta ta kashe su, na ga gawarwakin mutane bakwai.
“ Akwai kuma mutane da yawa wadanda suka samu raunukaa n dauke su cikin wata babbar mota zuwa asibitin dake kusa.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na jihar Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuar al’amarin.
Y kuma ci gaba da bayanin cewar an samu ga wadanda kuma Likitoci sun tabbatar da cewar sun mutune bakwai ne suka mutuwr mutane bakwai, sai kuma adana al’amarin nasu ba mai ahala bane, an tura su wasu asibitoci. Kamar asibitin koyarwa na jami’ar Nnewi.
“ Bugu da kari kuma daga cikin mutanen bakwai da suka rasu, an kai mutane uku dakin ajiye gawa na Amaku, sai kuma inda ake ajiye gaarwaki na, biyu kuma a Regina Caeli Hospita sai kuma sauran biyun a asibitin Piston inda ake ake ajiya gawa.
“ An dai samu kawo karshen shi al’amarin, duk kuma wasu abubuan da suka kawo cikas duk an gyara su.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!