Connect with us

MANYAN LABARAI

Idan Ba A Soke Zaben Zamfara Ba Zai Kawo Rigima –Jam’iyyun Adawa

Published

on

Jam’iyyuka adawa da ke cikin jihar Zamfara, sun tabbatar da cewa idan hukumar zaben ta kasa ba ta rushe zaben da ya gudana a makan da ya wuce na Shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya ba da ke cike da magudi, lalllai za a yi rigima.
Shugaban hadakar jam’iyyun adawa, dan takarar Gwamna a jam’iyyar Apga Alhaji Sani Abdullahi Wamban Shinkafi ne ya tabbatar da haka a dakin taron Wakilai kafafen yada labarai da ke Fadama a Gusau Baban birnin jihar Zamfara.
Shugaban hadakar ya bayyana cewa suna da tabbacin tun a ranar jajiberin zaben ne aka shirya wannan makircin yin magudi a hedikwatar ‘yan sanda da ke jihar, da Kwamishinan ‘yan sanda ya jagoranta Celestine Okoye da Kwamishiniyar zabe na jihar Dakta Asamau mai Kudi da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Honarabul Lawali Gamdon Kaura da Sakatarensa Honarabul Sani Mono kuma na je hedikwatar a lokacin aka hana ni Shiga a she akwai makircin da suke kullawa, a nan ne na nemi ganin kwamishinan, sai ya turo mini mataimakinsa a kan in fada masa abin da ke tafe da ni ni kuma na tsaya kai da fata na ce shi nake son gani. Shi ya sa ya fito ya saurare ni kuma na tabbatar masa da cewa “Ba mu yarda da canza kayan zabe ba da Kwamishiniyar ke son yi, nan dai na fada masa korafin amma babu wani mataki da ya dauka.
Haka kuma runfunan zabe an saci akwatina, an yi amfani da mazabun ‘yan gudun hijira da Naira dari biyar da dubu daya don a zabi ‘yan takara gwamnati da kudin gwamnati.
Kuma an kama mutane dumu-dumu sun kulle daki suna dangwale kuri’u kuma babu matakin daga Hukumar zabe da jami’an tsaro wannan ya tabbatar da cewa kitsa wannan makircin aka yi don haka mu jam’iyyu adawa ba za mu lamuncin wannan ta’addancin ba.
A kan huka muke kira ga Sufeto janar na ‘yansand da ya gaggauta dauke Kwamishinansa daga jihar Zamfara da ita kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta kori Kwamishiniyar zaben jihar don ba ta cancanci wannan aikin ba.
Wamban Shinkafin a madadin Shugaban jam’iyyun adawa sun dau alwashi bin umarni da Shugaban kasa ya bada na ganin bayan duk wanda ya saci akwati ko ya nemi kawo magudin zabe a jihar Zamfara, a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha mai zuwa.
Gamayyar jam’iyyun sun hada da Jam’iyyar PDP,Apga ,NRM ,ADC,YPP ,ACCORD, ABP, da sauransu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: