Connect with us

LABARAI

Dambarwar Siyasar Adamawa: Umurnin Kotu Ba Zai Hana Mu Gudanar Da Zabe Ba –INEC

Published

on

Hukumar zabe ta kasa INEC a jihar Adamawa, ta ce babu wani umurnin kotu da zai hana ta gudanar da zaben cike gurbi a runfunan kada kuri’a 44, dake fadin jihar, domin bayyana dan takarar da ya lashe zaben kujerar gwamna a jihar.
Wannan bayanin ya biyo bayan bukatar haka da dan takarar kujerar gwamnan jam’iyyar MRDD Mista Eric Dollars ya’yi, bisa zargin rashin lika tambarin jam’iyyarsa (Logo) a zaben da hukumar INEC ta gudanar ranar Asabar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan wannan batu shugaban hukumar zabe INEC a jihar Barista Kasim Gaidam, ya ce “Kodayake ba mu da wani labarin wani umurnin kotu, amma bari na shaida maka umurnin kotu ba zai dakatar da kowani zabe ba.
“sashi na 87 sakin layi na 10, na kundin dokar zabe ya bada cikakken bayani, ‘Babu abu da yake ikon kotu ta dakatar da zaben fid da gwanin da aka rike ko babban zaben gama-gari, ko kuma ci gaba da wanda aka faro’ karkashin wannan doka duk wani umurnin kotu ba zai yi aiki ba” in ji Gaidam.
Dama dai mai shari’a Abdul’Aziz Waziri, na babbar kotun jihar ya bada umurnin wucin-gadi ga hukumar zabe INEC game da gudanar da zaben wucin-gadi a runfuna 44 da zata sake zabe a cikinsu ranar 23/3/2019, domin ba’ayi zabe a wuraren ba.
Umurnin kotun dai ya biyo bayan gudanar da zaben kujerar gwamna da hukumar zabe INEC ta yi ranar 9/3/2019, ba tare da tambarin jam’iyyar Mobement for the Restoration and Defense of Democracy (MRRD), da dan takararta Eric Dollars, da ya garzaya kotu kan cewa ta hana zaben sake zabe a rumfuna 44 sai an shigar da tambarin jam’iyyarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!