Connect with us

SIYASA

Girmama Ra’ayin Juna Zai Taimakawa Gudanar Da Zabe Cikin Lumana, inji Auwal Abubakar Darma

Published

on

An ja hankalin al’ummar jihar Kano a kan girmama ra’ayin juna hakan zai taimakawa gudanar da zaben cike gibi da za a yi karashen na Gwamna a wasu mazabu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya ba tare da hatsaniya ba.Wani dattijo a jihar Kano, Malam Auwalu Abubakar Sulaiman Darma ya yi wannan nasihar a kan zaben da ke gabatowa na Asabar 23 ga wannan watan.
Ya yi nuni da cewa zabin shugaba abu ne me muhimmanci a Musulunci ya kuma a jiye hanya da za a yi zaben shugaba a lokacin sahabbai an zabi shugabanni takai tsaye data shawara da ta sauran hanyoyi. Mutanen jihar Kano Musulmi ne kuma suna da girma a idon yan kasar nan duk abinda suka yi mai kyau yana shafar yan Nijeriya haka ma akasin hakan don haka duk abinda aka yi mara dadi asara zai zama ga harkar kasuwanci da yara da ake dasu da masu zuwa nana gaba.
Malam Auwal Abubakar Darma ya ce, harkar zabe ba yaki bane ko yaki ne idan aka sami nasara a kan wani, wanda bai samu ba hakura yake, anyi zabuka da yawa ya wuce wanda bai nasara baya hakura anga irin daukaka da Allah ya bashi don haka ya kamata a dauka zabe wata gwagwarmayace tsakanin yan’uwa shakikai wanda dayane zai samu a cikinsu, wanda Allah ya kaddara shi ne, to Allah yasan dalilin da yasa ya zabi wane da dalilin da yasa bai zabi wane ba.Wanda ya yi nasara da wanda bai yi ba su dauki kansu a matsayin yan’uwa domin dama manufar ita ce bautawa al’ummar jihar Kano a hada hannu a dafawa ci gabansu.
Ya kara da cewa duk abinda za a samu na rashi jin dadi matsayin Kano da addininta da al’adarta za a kalla sai yarfe ya koma a kan su, dan haka wannan takara da ake na Gwamna a dauka takara ce tsakanin Hasan da Husaini duk wanda ya yi nasara a taru a bashi goyon baya, domin yanda ake harkar zabe kowa da ra’ayinsa da ba za a hana shi ba,hakan shine damakwaradiyya, ra’ayin wani bazai tilasta na wani ba. A baya lokacin NPN da PRP an yi irin wannan da aka yi zabe komai ya wuce saboda haka ayi koyi da baya a dauka duk abinda za a yi kasa akewa da ci gaban al’umma mabiya su sani ba fadane tsakanin wane da wane ba abu ne na kowa yana da ra’ayinsa a kalli juna a matsayin yan’uwa ba zance ne na fada ko tada jijiyar wuya ko rike makami ba,an riga an wuce wannan a tarihin Duniya gaba daya, dabbanci ne na jahiliyya wani ya ce, zai yaki wani a kan ra a yi.
Malam Auwalu Abubakar Darma ya kara da jan hankalin al’ummar Kano da cewa duk gaba dayansu yan’uwane Hausa Fulani saboda haka a kalli a rika kallon kai a matsayin yan’uwa duk wani abu daya taso na siyasa ko za a yi zabe a rika mutunta kowa da ra’ayinsa, sannan kuma al’umma da za’a yi zabe a wurarensu su yi zabe cikin nuna yan’uwantaka da girmama juna hakan zai bada dama a yi zabe lafiya wanda ya yi nasara a bashi goyon baya dan ci gaban al’ummar Kano.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!