Connect with us

TATTAUNAWA

Gwamna Gaidam Ya Yi Kokarin Cike Gibin Karancin Ma’aikatan Lafiya A Yobe – Dr. Hamisu

Published

on

DR. HAMISU MAIMUSA, shi ne shugaban (Probost) na makarantar ‘College of Health Science and Technology, Nguru a jihar Yobe, ya bayyana yadda Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi kokarii wajen inganta kiwon lafiya, ta hanyar inganta makarantun horar da ma’aikatan lafiya da sauran batutuwa a tattaunawarsa da wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD MAITELA, a Yobe. Ga hirar kamar yadda ta ke:

Yallabai za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatu.
Da farko dai, sunana Dr. Hamisu Maimusa, shugaban (Probost) na College of Health Science and Technology, Nguru da ke nan jihar Yobe.

To wadanne kwasa-kwasai ne wannan kwalejin ke yi?
A takaice dai, kamar yadda sunan ya nuna kan cewa, wannan ‘College of Health Science and Technology’ ce, wadda da farko a ka santa da ‘School of Health Technology’, wanda a wancan lokacin ba ta bunkasa kamar a haka ba. Saboda a wancan lokacin a na koyar da kwas bai wuce guda biyu ba kawai.
To daga nan kuma, a yanzu wannan makarantar ta kai shekaru 19 da kafuwa, ta fara a shekarar 1999, a matsayin school of health technology, Nguru. A lokacin bai wuce kwas biyu a ke yi ba: Community Health da Enbironmental Health, ana haka har zuwa 2004, a lokacin da mutanen hukuma mai kula tsarin koyar da community health su ka zo batun tantance kwasakwasan, dangane da yadda tsarin ke gudana, wanda suka fahimci akwai wasu ka’idojin da ba a cika ba; gine-gine da kayan aiki, sai suka janye batun yiwa kwas din ‘Community Health’ rijistar.
Lamarin da ya jawo aka bar makarantar da kwas daya kawai: Enbironmental Health apartment kawai, a 2004. To, ganin haka ne ya sa Maigirma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam, ya ga cewa babban abinda yakamata ace dan adam ya samu a rayuwar sa, bayan an halicce shi, da ya wuce inganta kiwon lafiyar sa. Shi ne ya yi yunkuri wajen saka dokar-ta-baci a sha’anin ilimi da kiwon lafiya a jihar Yobe.
Matakin da ya shafi ba ma a wannan kwalejin ba kadai, ya kama tun daga babbar asibitin koyarwa- ta jami’ar jihar Yobe, asibitin kwararru dake Damaturu, sai manyan asibitocin jihar baki daya (General Hospitals) tare da makarantun da ke horas da kwararrun ma’aikatan jinya- School of Nursing, da makamantan su, wanda gwamnati ta sake inganta su, domin bayar da gudumawar da ake bukata a sha’anin kiwon lafiyar al’ummar jihar Yobe kuma da cika ka’idojin da hukumomin rijistar kwasakwasan da ake da bukata, kamar takwarorin su a kasa.
Kuma aka yi kokarin canja makarantar daga School of Health Technology zuwa College of Health Science Technology, Nguru- a hukumance, yayin da majalisar dokokin jihar Yobe ta amince da wannan matsayi, a cikin watan Junairun 2017.
Baya ga wannan kuma, a bisa ka’ida, ana sa tsammanin tunda makarantar ta koma kwaleji ta koyar da akalla kwasakwasai 9, irin su ‘community health’ da ‘enbironmental health’ da ‘Pharmacy’, ‘Dental’ da ‘Records’ da ‘medical lab’ da CEHW da JCEHW da EHA, AVT.
A lokacin an yunkuro domin samun ilimin kiwon lafiya mai karfi domin a samu yiwa wadannan kwasakwasan rijista, a 2004. Wanda mu kuma Allah ya kawo mu a wannan lokacin (2017) a matsayin shugaba bayan makarantar ta zama kwaleji. Wanda zuwan mu ke da wuya, bayan da muka ga kokarin da gwamnati ta yi shi ne mu kuma muka yi kokarin dawo da makarantar a zuwa nan; daga inda take a da.
Kuma bisa ga hakikanin gaskiya gwamnatin jihar Yobe ta yi rawar gani wajen samar da duk abinda kwaleji makamanciyar wannan ke bukata, da yanayin da zai kai ga samun nasarar yiwa wadannan kwasakwasan rijista. Daga cikin ci gaban da ta samar akwai gine-ginen da kowacce makaranta ke da bukata, kamar gina bangaren gudanarwa (Admin Block) da dakunan kwanan dalibai (Hostels) da nagartattun ajujuwan karatu da dakin bincike da nazari tare da zakin shan magani (clinic) da makamantan su, wanda aka yi su bisa ga inganci.
Ta dalilin wadannan, shi ne sai muka dauki matakai wajen karkiro da sabbin kwasakwasai kari daga biyun da ake dasu a da zuwa yadda yakamata. Wanda bayan zuwan mu sai muka mayar da kwas din HPE ta zama bangare mai zaman kanta hadi da biyun da ake dasu da (community health da enbironmental health). Daga nan ba mu yi kasa a gwiwa ba, sai muka samar da kwas din Pharmacy, Dental da Medical Record, Medical Laborotary, inda suka zama guda 7 kenan.
Sannan daga baya sai muka sake gayyato hukumar kula da community health department- wadanda da farko suka ki amincewa su yi rijistar kwas din a 2004, wanda kuma zuwan su ke da wuya; da suka ga ci gaban da muka yi wanda muka samu maki 82, a binciken tantancewar da suka yi mana, wanda kuma nan take suka ce sun bamu cikakken rijistar.
Wanda a karkashin wannan sashen sai muka dawo da kwas din CEHW da JCEHW tare da daukar sabbin daliban su da sauran kwasakwasan da muke dasu; wadanda na zayyana maka a baya. Daga nan kuma sai muka kara gayyato hukumomin da ke kula da su domin su zo su duba tare da yi wa kwasakwasan rijista; wanda na ‘Medical Lab’ sun zo kuma sun gamsu da abinda muke dashi a kasa, su ma na pharmacy sun zo tare da nuna amincewa da yadda tsarin da muke dashi; har wa yau na ‘Dental’ suma sun gamsu damu tare da yi mana rijistar, wanda yanzu yan ‘medical record’ ne muke dakon zuwan su- kuma muna da tabbacin suma zasu gamsu da tsarin da muke dashi.
Wanda a halin da ake ciki yanzu an yiwa kwas 7 rijista a wannan kwalejin- hudu sabbi sannan ga uku da muke dasu a baya. Amma kar ka manta muna gudanar da kwas 9 ne, wadanda suka kunshi Diploma da Certificate hadi da wasu na daban biyu- ka ga kwas 11 kenan.

Ta wanne tsari kuke gudanar da wadannan bangarori guda biyun; Diploma da Certificate?
A sashen kwas din community health, muna da tsare-tsare guda biyu; Diploma da Certificate. Diploma shi ne CHEW (community Health Edtension Workers), sannan da JCHEW a matsayin Certificate. Kuma amma certificate din kwalejin mu shekara biyu ne, ita kuma Diploma shekara uku, wanda ya sha bamban da sauran tsaruka, wadanda ake wata 9 ko shekaru 2. Saboda wanda yake da Certificate daga wannan kwalejin ya samu cikakkiyar kwarewa da ilimi daidai da mai Diploma a wasu makarantu.
Suma bangaren ‘enbironmental health’ a haka muke gudanar da tsarin; suna yin EVT (Enbironmental Health Technician) da EHA (Enbironmental Health Assistance) Diploma da Certificate.

Bisa wannan kokarin, kuna da kimanin dalibai nawa a wannan kwalejin?
Ka san mu muna da ka’idojin da tsarin da masu kula da wannan kwalejin suka tsara wajen daukar dalibai. Wajen sarin karatu da jarrabawa da kammala karatu da makamantan su. Wanda akwai hanyoyin da suke dashi wajen tantance kowanne dalibi tare da gudanar da tsare-tsare.
Misali sashen ‘enbironmental health’ suna daukar adadin dalibai 100, ne, EVT 100, EHA 100, HPE 100, Dental 100, Pharmacy 30, Medical Lab 50 zuwa 70, wanda a kowacce shekara muna daukar kimanin dalibai 650, shekarar karatu na biyu ma haka. Wanda da yake ba yanzu muka fara tafiyar da kwalejin ba, amma yanzu haka muna da kimanin dalibai 2400 zuwa 2500.

Wadanne matakai dalibi zai bi wajen samun zarafin shiga wannan kwaleji?
Yadda muke daukar dalibai shi ne, ta hanyar kafofin sadarwa na zamani, tare da bai wa kowa da kowa dama, ba dole sai dan jihar Yobe kadai ba. Kowanne dan Nijeriya yana da dama, muddin ya cika sharudda da ka’idojin bangarorin da muke dasu na cancantar shiga.
Duk da muna kula da yankuana da kason da yakamata su samu na adadin dalibai, amma kuma muna da kula ta musamman ga yankunan karkara da suke da karancin ma’aikatan lafiya, wajen basu dama, wajen farfado dasu a sha’anin kiwon lafiya.

Wacce gudumawa wannan kwalejin ke bayarwa wajen habaka sha’anin kiwon lafiya?
Kamar yadda na fada da farko, kan cewa a baya jihar Yobe muna da wagegen gibi dangance da ma’aikatan kiwon lafiya. Wanda kowacce karamar hukuma tana da asibiti da cibiyoyin kiwon lafiya, wanda suke bukatar ma’aikatan. Kuma abin bai tsaya a nan ba, ya hada da sauran jihohin da muke makwaftaka dasu.
Kuma wannan kwalejin ita kadai muke da ita a jihar Yobe wadda take bayar da irin wannan horon, wanda yanzu Alhamdullah mun kama hanyar warware wadannan matsaloli na karancin ma’aikatan kiwon lafiya a asibitocin mu, wanda idan ba haka muka yi ba, za mu ci gaba da fuskantar matsalolin.
Bugu da kari kuma, daga lokacin da aka kafa wannan kwalejin zuwa yau, ta taka muhimmiyar rawa a wannan bangare. Wanda a halin da ake ciki yanzu babu asibiti ko cibiyar kiwon lafiya, a kananan hukumomin jihar Yobe da babu daliban mu a ciki. Kuma haka abin zai ci gaba.

Me za ka ce dangane da kokarin gwamnatin jihar Yobe wajen inganta sha’anin kiwon lafiya?
Ai ba a cewa komai, dangane da zurfin tunanin Maigirma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam wajen yin hubbasar kyautata tsarin kiwon Lafiya. Wanda ya taka muhimmiyar rawa a bangaren kuma suk Nijeriya an yi masa wannan shaida, sannan abu ne a zahiri ba dodorido ba.
A lokacin gwamnatin sa ne tsarin kiwon lafiya a jihar Yobe ya bunkasa fiye da kowanne lokaci, kuma wannan shi ne abinda yakamata shugaba yayi tare da nuna kishin sa ga al’ummar sa, sannan kuma ya cancanci dukan yabo. Saboda ba domin kokarin sa ba da bamu kai ga cimma wadannan nasarorin ba.
Kuma mu na da burin hada hannu da karfe da gwamnati tare da al’ummar mu wajen ganin wannan kwalejin ta bunkasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!