Connect with us

WASANNI

’Yan Wasa Da Yawa Za Su Iya Barin Real Madrid

Published

on

Da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za su bar kungiyar a karshen wannan kakar bayan da shugaban kungiyar ya ware makudan kudade domin siyan sababbin ‘yan wasa kamar yadda kociyan Real Madrid Zidane ya bayyana.
Tuni Real Madrid ta siyi dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta FC Porto Elder Militao akan kudi fam miliyan 42 kuma ana cigaba da danganta kungiyar da dan wasa Edin Hazard dana Manchester United Paul Pogba.
Sai dai banda sababbin ‘yan wasan da Real Madrid zata siya akwai kuma wasu da yawa daga cikin ‘yan wasan tawagar da zasu iya barin kungiyar domin su bawa sababbin da za’a kawo waje domin buga wasa kamar yadda Zidane ya bayyana.
Amma anyiwa Zidane Magana akan dan wasan tsakiyar kungiyar, Isco, inda Zidane ya tabbatar da cewa akwai wasu daga cikin ‘yan wasan da kungiyar bazata siyar dasu ba saboda sunada amfani sosai.
Sannan ya ce akwai kungiyoyi da yawa da suke neman siyan ‘yan wasan kungiyar kuma Isco yana daya daga cikinsu saboda haka zasu cigaba da Magana da dan wasan a karshen kaka domin ganin yadda za ta kasance.
Real Madrid dai anyi waje da ita daga gasar cin kofin zakarun turai a zagayen falan daya sannan kuma kungiyar Barcelona tayi waje da ita a gasar cin kofin Copa Del Rey har ila yau kuma maki 12 ne tsakaninsu da barcelona wadda take mataki na daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!