Connect with us

RAHOTANNI

Zargin Kin Biyan Haraji: Kotu Ta Jaddada Warantin Kama Okocha

Published

on

A ranar Litinin ne, wata babbar kotu da ke Igbosere, a Legas, ta tabbatar da warantin da tun da farko ta bayar a ranar 29 ga watan Janairu, na kamun tsohon Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya, Augustine Okocha, a kan zargin sa da kin biyan haraji.
Mai Shari’a Adedayo Akintoye ne ya tabbatar da warantin a bisa neman hakan da mai gabatar da kara na Jihar Legas, Mista Yusuf Sule, ya yi.
Sule ya shaidawa kotun cewa, Okocha, har yanzun bai bi shawarar daidaitawa a wajen kotun da kotun ta ba shi damar hakan ba tun da farko a kan ya sauke nauyin harajin da ke kansa na shekarar 2017.
Mai gabatar da karan ya ce, Okocha, ya kasa halartar kotun tun daga ranar 5 ga watan Oktoba, 2017, ranar da aka fara kiran shari’ar.
Sai dai kuma, Okocha ba shi a cikin kotun, bai kuma aiko da wani Lauya da zai tsaya ma shi ba.
Sule ya kuma ce, Okochan ya yi magana da hukumar tara kudaden haraji ta Jihar Legas.
Ya ce, wanda ake karan yana kokarin daidaitawa, amma dai har yanzun bai biya ko sisi ba.
“A kan hakan, muna neman a sanya mana wata ranar ta daban.”
Da yake amincewa da bukatar mai gabatar da karan, Mai Shari’a Akintoye, ya yi hukunci da cewa, “Warantin kamun zai ci gaba da kasancewa a kan wanda ake karan.
“An dage sauraron shari’ar har sai 28 ga watan Mayu.”
Tun da farko, mai gabatar da karan ya gabatar da tuhumomi uku ne a kan Okocha din a ranar 6 ga watan Yuni, 2017, yana tuhumar sa da laifukan:
“Kasa biyan harajin sa ga hukumar tara kudaden haraji ta LIRS.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!