Connect with us

TATTAUNAWA

Gwamnatin Tambuwal Za Ta Bai Wa Marada Kunya A Karo Na Biyu – Hon. Bashire

Published

on

HON. ABUBAKAR ZAKI BASHIRE Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal ne kuma fitaccen babban jigon dan siyasa ne wanda yana sahun gaba a cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawar samun nasarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a karo na biyu. A wannan tattaunawar da ya yi da LEADERSHIP A YAU LAHADI ya bayyana alkiblar da Gwamnatin Tambuwal za ta dosa a 2019-2023 da batun shari’ar zaben Gwamna da irin romon mulkin Dimokuradiyya da al’ummar Jihar za su sha a wa’adin mulkin sabuwar Gwamnatin Jihar a karo na biyu kamar yadda ya bayyanawa wakilinmu SHARFADDEEN SIDI UMAR DOGON-DAJI.

Honarabul ya ya za ka bayyana nasarar da Gwamma Aminu Waziri Tambuwal ya samu ta hanyar galaba kan jam’iyyar APC a zaben da ya gabata?
Alhamdulillahi gagarumar nasarar da Mai Girma Gwamma Aminu Waziri Tambuwal ya samu a Babban Zaben 2019 a matsayin wanda ya lashe zabe a karo na biyu a jam’iyyarmu ta PDP nasara ce daga Allah madaukakin Sarki wanda a cikin ikonsa ya nufa ya kuma kaddari Mutawallen Sakkwato da sake zama kan kujerar ragamar mulkin wannan jihar mai albarka a shekaru hudu masu zuwa.
Don haka a kodayaushe muke kara mika cikakkiyar godiyar mu ga Allah mai kowa mai kowa a kan wannan nasara, daukaka da ni’imar da ya yi mana wadda nasara ce ba ta mutum daya ko daidaikun mutane ba nasara ce ta jimlatan din al’ummar Jihar Sakkwato wadanda suka roki ubangiji ya ba su shugaba nagari wanda zai bunkasa jihar su tare da kai ta a tudun mun tsira. Alhamdulillahi muna kara godiya ga Allah da dukkanin wadanda suka bada ko wace irin gudunmuwa kan wannan nasarar.
Me za ka ce kan kalubalantar zaben da APC ke yi tare da ikirarin cewar dan takarar ta ne ya samu galaba?
Ba zan so in yi dogon tsokaci kan maganar da ke gaban kotu ba, amma dai tabbataccen abu shi ne Mutawalle ne Sakkwatawa masu kishi, sanin ya kamata da hangen nesa suka zazzagawa ruwan kuri’un su saboda gamsuwa da salon mulkinsa da amanna da ittafakin zai sake gudanar da mulki nagari a karo na biyu.
Duk dai yadda ta kaya In sha Allah gaskiya za ta yi halinta, saboda kamar yadda kowa ya sani tun ran gini tun ran zane haka ma ramin karya ai kurarre ne, wanda Allah ya zaba ya riga ya zabe shi don haka maimakon bata itace wajen dafuwar kaho abin da ya kamata kawai shi ne jam’iyyar APC ta bayar da hadin kai da goyon baya ga wannan Gwamnatin kamar yadda Mai Girma Gwamma ya bukata domin hada hannu a ciyar da wannan jihar a gaba.

Bayan samun nasarar Tambuwal a karo na biyu, ta ina kake ganin zai fara jan zaren mulki a wannan sabon zangon?
Gwamnatin Mai Girma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Gwamnati ce ta jama’a wadda jama’a suka yi ruwa da tsaki wajen kafuwar ta don haka sabuwar Gwamnati a tafin hannun sa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen kyautata jin dadi da inganta rayuwar al’umma. Daga 2019- 2023 al’ummar wannan jihar za su shaidi ingantaccen sahihin mulki na adalci, wanzar da zaman lafiya, habaka ci-gaban jiha da al’umma bakidaya.
Mai Girma Gwamna da kansa ya bayyana cewar Gwamnatin sa za ta bayar da fifiko ga kammala ayyukan da ta assasa tare da kirikiro sababbin ayyuka wadanda za su yi tasiri da alfanu ga al’umma. Ayyukan inganta sha’anin ilimi wanda Gwamnatin Mutawalle ta kafawa dokar daukin gaggawa a farkon hawanta mulki saboda tasirinsa na sahun farko na ababen da za su samu kulawar musamman kamar yadda za a bunkasa fannin kiyon lafiya, gina asibitoci, samar da kayan aiki da daukar ma’aikata. Fannonin kawar da fatara ta hanyar karfafawa mata da matasa da inganta hanyoyin samar da kudin shiga ta hanyar bunkasa tattalin arzikin jiha duka abubuwa ne da Gwamnatin Mutawalle za ta bayar da himma tare da baiwa marada kunya da yardar Allah.

Me za ka ce kan wadanda ke da ra’ayin Tambuwal bai taka rawar da ta kamata ba a wa’adinsa na farko?
Dama ai Hausawa na cewa ra’ayin riga. Ba ka tunanin wanda ke adawar siyasa da kai ya fadi alhairin ka amma komai tsatsar hassadar dan adawa ya san Tambuwal ya shimfida muhimman ayyukan alhairi a wannan jiha. A iya sanin al’ummar Jihar Sakkwato Mai Girma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya taka muhimmiyar rawar gani wajen canza fasali da alkiblar mulkin Jihar Sakkwato.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!