Connect with us

WASANNI

Manchester United Na Zawarcin Pepe Da Rabiot

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Lille, Nicolas Pepe da kuma dan wasan tsakiyar Paris Saint German, Adrien Rabiot, dan kasar Faransa domin su koma kungiyar.

Tauraruwar Pepe dai tana haskawa a wannan kakar bayan daya zura kwallaye 21 cikin wasanni 39 daya bugawa kungiyarsa ta Lille sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye 12 wanda hakan yasa manyan kungiyoyi a nahiyar turai suka fara zawarcinsa.

Kungiyoyin Arsenal da Bayern Munchen ma dai suna zawarcin dan wasan dan asalin kasar Ibory Coast yayinda kuma wasu rahotanni suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta PSG ta fara tattaunawa da dan wasan akan komawarsa zakarun na kasar Faransa.

Har ila yau, wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta shirya kashe kudi fam miliyan 45 domin siyan dan wasan wanda ake ganin zai taimakawa kungiyar sosai a kakar wasa mai zuwa.

Har ila yau, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United  ta fara zawarcin dan wasan tsakiyar kungiyar Paris Saint German, dan wasan kasar Faransa, Adrien Rabiot, wanda zai bar kungiyar tasa a karshen wannan kakar.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana zawarcin Rabiot, wanda a kwanakin baya aka bayyana cewa ta kusa kammala cinikinsa bayan ya buga wasanni sama da 220 kuma rabon da ya bugawa PSG wasa tun watan Disambar shekarar data gabata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!