Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Sace Surukar Gwamna Masari

Published

on

‘Yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kama wadanda ake zargi suna da hannu a yin garkuwa, da mahaifiyar matar gwamnan jihar Aminu Bello Masari a watan Maris.
Mai magana da yawun rundunar,  SP Gambo Isah, ne ya tabbatar da hakan sannan ya kara da cewa an tura wadanda ake zargin zuwa Abuja don ci gaba da gudanar da bincike.
Ya ce,  ‘Gaskiya ne mun kama mutane da dama da muke zargi suna da hannu a kan lamarin da ya faru kuma mun tura su zuwa Abuja.  Shelkwatar ‘yan sanda za ta ci gaba da gudanar da buncike akan su.
An sace tare da yin garkuwa da Hajiya  Maistiyari mai shekaru 80 wadda mahaifiya ce ga Binta,  matar gwamna Masari, sannan an sake ta bayan wasu kwanaki kalilan.
Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa har yanzu dai babu wani ci gaba don gane da binciken garkuwa da Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar. Amma ya tabbatar wa da mutane cewa rundunar tana aiki tukuru don ganin cewa an sako shi.
Har ila yau, Isah ya kara da cewa rundunar sun kama wasu bata gari a yunkurin su na ganin an rage aikata laifuka a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!