Connect with us

ADABI

Yawan Karanta Littattafan Hausa Ya Sa Ni Sha’awar Rubuta Littafi — Rahmatu

Published

on

Za Mu So Ki Gbatar Da Kanki Ga Masu Karatunmu

Sunana Rahmatu Hassan Muhammad.

An haife ni jihar Neja, garin Minna Kuma nan na taso na girma, sannan anan na yi karatuna kama daga firamare har zuwa difuloma inda na dakata da karatu nake nan, sannan na kama kasuwanci.

Wane dalilin ya sa kika fara rubuta littafi ?

Gaskiya na kasance mai yawan karance-karance Kama daga littafan Hausa da na Ingilishi har na Nupe, sannan da ma tun a makaranta nakan rubuta gajerun labarai don kawayena da abokai su karanta, amma da yake ban dauke shi da muhimmanci ba, sai abin ya fitar min a rai.

Bayan na gama karatuna na zo ina zaman gida, ban da abin yi sai “chatting” leka wannan “group” yau gobe waccan har Allah ya yi na shiga “Elokuence writers group”, na kasance makaranciya a cikin “group” din, amma duk da hakan nakan tsaya in lura da yawan kurakuren da marubuta ke samu, wanda ya yi silar jefa mutane da dama cikin rudani, kamar yawan zuzuta mata da samarin “nobel” hakan ya soma damuna amma na rasa hanyar shawo kan matsalar.

Cikin hakan na shiga wani “group Kueen nerdy nobels”, sai Kuma na fara sha’awar ni ma in rubuta littafi, in gwada tawa bajintar duk da ina ta jin kamar ba zan iya ba, kasancewa ta Banufiya ban gama jin Hausa ba.

Kwatsam rana daya sai na gwada rubuta wani gajeren labari na aika, sai labarin ya samu karbuwa jin dadin karbuwar wannan labara nawa, sai na ga ashe zan iya, da haka na fara.

Za ki kai kamar shekara nawa da fara rubutun?

Gaskiya ban dade da fara rubutu ba, amma dai ina ganin na fara a sa’a, saboda ina jin dadin yinsa kuma yana samun karbuwa wajen mutane.

Wane littafi kika fara rubuta wa?

Littafin da na fara rubutawa shi ne “ita ce”.

Wane sako littafin ke dauke da shi?

Na yi la’akari da ra’ayin mutane ne, idan har kana son ka ja hankalin dole sai ka samu wani abu muhimmi da za ka ba su.

Labarin ita ce ya kasance ya sanya musu kwadayin son sanin ita wa, mene ne game da ita, me ake nufi da ita ce ko me ta yi, saboda haka Kin ga karamin labari ma  ya sa  tambayoyi da dama cikin zukatan makaranta, sannan cikin hakan na yi amfani da damar don ankarar da su irin kkalubalen da wasu ke fuskanta a rayuwa, da kuma irin rayuwar shirka da wasu suke fama da shi har yanzu a wasu bangaren duniya haka kuma irin jahilci da wasu ke fama da shi da nuna son zuciya karara ko da ga y’aya’nsu ne da suka haifa.

Shin ko kin taba cin karo da wani kalubale daga fara rubutun ki kawo yanzu?

Eh, ba zan ce a’a ba, domin har mutane biyu suka neni su yi min bayani kan cewa ina samun kurakurai gun bambanta wasu harufa kamar kofa ko sanyi haka toh dai na fahimtar da su ni ba Bahaushiya ba ce kuma dole a samu hakan amma da yardar Allah a hankali ni ma zan gane bambancinsu iya matsalar da na taba samu ke nan.

Shin ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta daga masu karatu har ma da masu rubutun?

Wanda ba zaki taba mantawa da shi ba.

A’a gaskiya ban taba fuskantar kowane kalubale ba daga wajen su sai ma karfafa min gwiwa da suke gaskiya Masha Allah

Me za ki iya cewa, dangane da halayyar masu rubutu, saboda za ki ji wasu na cewa, sun fiye jiji da kai ko wulakanci da sauran su, shin duka marubutan ne haka, ko kuma wasu ne ke bata wasu?

Gaskiya tun da na fara rubutu ba kowace marubuciya ko marubuci nake saurin shiga sha’aninsa ba, amma abin da na lura shi ne, na kara samun kusancinsu domin har wadanda ban sani ba sukan bi ni su min barka tare da karfafa min gwiwa, saboda haka ni fa ban tunanin marubuta suna da girman kai kamar yadda ake fada sai dai idan dama makarantan suke nunawa jijji da kai amma ni fa ko da na fara rubutu ina da kyakkyawara fahimta da marubuta.

Wane lokaci kika fi jin dadin rubutu?

Kowane lokaci ban da takaimamen lokacin da na fi jin dadi, jin dadina shi ne lokacin da tunain ya ya zo min a kai kawai sai in lalubi wayata in fara rubutu, idan kuma na ji kan ya dau zafi in yi in dakata.

Wace marubuciyar ce ta fi burge ki?

Ni ban da marubuciyar da ta shiga raina balle har ta burge ni da wani abu, amma dai akwai littafin da na taba karanta na “Amrah nake so” gaskiya na yaba da kokarin marubuciyar gun hada wannan labarin duk da na manta sunanta yanzu amma gaskiya na yaba da irin gudummowarta kan addinin Musulinci domin duk wanda zai karanta wannan littafi hakika zai kara kusanci ga Allah da Kuma baya-baya kan lamuran duniya da abin da ke cikinta, Kuma littafin da na fara karanta shi ne “Tawa Ta Same Ni” shi ma dai ban rike sunan marubuciyar ba.

Mene ne burinki a rayuwa dangane da rubutunki?

Da dai ban da ma niyyar ci gaba da rubutu amma irin goyon bayan da nake samu daga abokai da kuma makusanta, irin hura kannan kin gane ai sai na fara jin zan yi iya kokarina ganin cewa rubutuna ya kai fiye da inda nake zato, zan so a ce ta dalilin rubuce-rubucena sunana ya shahara ta kowane gefen da ya tabo shafin marubuta za a ji ni.

Shin kina da aure?

A’a ban da aure.

Wace shawara za ki ba marubuta, har ma da masu karatu?

Shawara na ga marubuta it ace, su sassauta irin fassalin da suke bai wa mata da maza a cikin littafinsu, sannan kuma a ce mutum ya tara komai ai hakan bai yiwuwa, wanda shi ne dalilin yawan mata ka ga yanzu ba su son tarayya da dan talaka haka ma mazan ka ga kiri-kiri suna da masu sonsu amma su kafe ala-dole sai irin macen nobel sai ka ce matan aljanna, gaskiya a rage domin hakan ba karamar masifa ce ba cikinmu, Kuma a hada karfi da karfe a taimakawa juna, duk inda ka ga dan’uwanka ya samu kuskure a gyara ban da tsangwama ko zagon kasa.

Sannan makaranta su gane cewa yawancin abubuwa ana zuzuta su ne a littafi. Saboda haka wani lokacin rayuwa ta zahiri kan bambanta da ta littafi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!