Connect with us

TATTAUNAWA

Bayan Shekara 50 Da Kafuwa: Cibiyar Koyar Da Ilimin Manya Ta Yaye Dalibai Da Dubu Dari Biyu A Kano —Barden Madaki

Published

on

A Tattaunawarsu da  jaridar LEADESHIP A YAU LAHADI, Shugaban Cibiyar koyar da ilimin manya da ke makarantar Shahuci  cikin birnin AHAJI GARBA BABAN LADI SATATIMA (Barden Madakin Kano) ya bayyanawa cewa, daga fara karatu a wannan Cibiya zuwa wannan lokacin,  ta yaye dalibai sama da dubu dari biyu, wadanda suka ci gaba da gudanar da karatu da sana’o’i a fannin rayuwar yau da kullum. Yanzu haka Baban Ladi shi ne mataimakin shugaban kungiyar iyaye da malaman makaranta na jihar Kano. Sannan Barde ya bayar da takaitaccen tarihin wannan Cibiya da nasarorin da ya samu a wannan Cibiya.

Masu karatunmu za su so ka gabatar da kanka, don sanin tare da muke a wannan shafi, na wannan makon.

Sunana Alhaji Garba Baban Ladi Satatima Barden Madakin Kano. Ni ne na kafa kuma nake ci gaba da gudanar da koyar da ilimin manya a makarantar Masallaci da ke Shahici, wanda zuwa wannan lokaci na shafe sama da shekara hamsin ina gudanar da wannan makaranta, wadda kuma na samu nasarar koyar da dalbai masu dimbin yawa a ciki da wajen jihar Kano, wanda bisa kiyasi sun kai sama da dubu dari biyu.

Za mu so ka bayyanawa masu karatunmu takaitaccen tarihinka.

An haifi ni  a cikin birnin Kano ranar 21 ga watan Afirilu na shekara ta 1947 a unguwar Satatima. An fi sanina da Barden Madakin Kano kuma ana yi mini lakabi da Babban Malam, saboda kawo habakar ilimin manya da na yi a jihar Kano da ma Nijeriya baki daya.

Na fara kara karatuna na farko a Isalamiyyar Yolawa daga shekara ta 1955 zuwa 1957. Sannan ya yi makarantar firamare da ke Kofar Kudu daga shekara ta 1958 zuwa 1964, sannan na wuce zuwa makarantar firamare ta Kuka a shekara ta 1964.

Daga nan na shiga makarantar Igbo Union Grammer School  da Ke Kano, a sashin koyon ilimin manya daga shekara ta 1964 zuwa 1966. Na je makarantar koyarda ma’aikat . Sannan kuma na wuce Shool of Management Studies da ke Kano daga shekara ta 1977 zuwa 1978, sai kuma jami’ar Ahmadu Bello daga shekara ta 1985 zuwa 1980.

Na halarci kwasa-kwasai da dama a cikin da wajen jihar Kano, haka kuma na je taron karawa juna sani a lokuta daban-daban wadanda suka shafi fannoni daban-daban na ilimi, wadanda suka san a kara samun kwarewa da gogewa a rayuwar yau da kullum.

Na rike mukamai daban-daban, na yi aiki a ofishin hakimin Waje, na yi aikin karbar haraji a ofishin hakimin waje. Sannan na yi aiki da Hukumar yada ilimin manya ta jihar Kano.

Wadanne abubuwa za ka bayyanawa masu karatunmu a matsayin nasarar da ka samu sakamakon kafa wannan Cibiya ta ilimin manya?

Babban nasara da kullum nake alfari da ita, ita ce, dorewar wannan Cibiya, tun daga lokacin da aka fara wannan karatu sama da shekara hamsin, har zuwa wannan lokaci kullum ci gaba muke samu.

Abu na biyu kuma shi ne, wannan Cibiya ta koyar da daliban da ba za a iya sannin yawansu ba, sai dai bisa kiyasi ana zaton sun haura dubu dari biyu wadanda suka fantsama kuma suke bayar da gudummowa ga al’umma a fannin rayuwarsu ta yau da kullum, a dukkan fadin kasar nan.

Haka wata babban nasarar da na samu ita ce ta cewa, a halin yanzu wannan makaranta ta zama Cibiyar bincike a kan ilimin manya, saboda haka muna samun masu bincike a kan ilimin manya daga jami’o’in da ke ciki da wajen kasar nan, wannan ce ma ta sa a kwanakin baya Sashin nazarin ilimin manya na jami’ar Legas ya karrama ni da digirin girmamawa na Dakta.

Karin wani abin alfarina da farin cikin da nake yi dangane da wannan makaranta shi ne, ta samar  da ayyuka ga dimbin al’ummar da ban san adadinsu ba. Dalibai da yawa da suka gama wannan makaranta sun samu ayyukan karkashin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, wasu kuma sun rungumi sana’o’i da kasuwanci, saboda haka, kusan kowane bangare musamman a nan jihar Kano in ka bincika za ka ga akwai dalibin wannan makranta da yake bayar da gudummowa,

Yanzu haka akwai dalibai dubu uku da dari biyar  da suka fito daga kananan hukumomi takwas da ke kusa da makarantar  wadanda ke iya zuwa wannan makaranta daga cikin kananan hukumomi arba’in da hudu da ke fadin jihar Kano.

Daga cikin fitattun mutanen da makarantar ta koyawa karatu akwai, Dakta Ibrahim Kunya Kwamishinan muhalli na farko a jihar Kano, sai Alhaji  Auwalu Munjibir  Tsohon alkalin alkalai na jihar Kano sannan akwai Dakta Abubakar Nasidi Goron Dutse, Malami a jami’ar Bayero ta Kano, sai Hajiya Halima Sabo Ma’aikaciya a  hukumar WHO da Sheik Tijjani Bala Kalarawi, da Ado Ahmad Gidan Dabinai da marigayi Sheik Jafar Mahmoud Adam da sauransu.

Ko za ka bayyanawa masu karatunmu yadda tsarin koyarwa yake a wannan makaranta?

Wannan makaranta, ta ilimin manya na koyarwa a matakin farko da matakin tsakiya da share fagen shiga manyan makarantu da kuma ilimn sana’o’i,  makarantar na da malamai guda dari biyu da goma.

Wadanne kalubale kake fuskanta dangane da wannan makaranta?

Gaskiya duk da cewa, kowane abu a rayuwa na tattare da irin kalubalensa, sai dai kalubalen wani yakan fin a wani, amma dai cikin ikon Allah da hadin kan da muke samu daga dalibai da kuma taimakon da muke samu daga wasu manyan mutane za mu iya cewa, muna da saukin kalubale.

Wane kira kake da shi ga al’ummar jihar Kano da ma na kaaa baki daya?

Babban sakona ga al’ummar jihar Kano da ma na ko’ina a fadin duniya, shi ne su rungumi ilimi domin shi ne mafita a rayuwar duniya da kuma lahira. Kuma zan dada tunatar da mutane a kana bin da suka sani, cewa, yawan shekaru bay a hana a koyi ilimi, wannan makaranta ta mu ta isa ta zama babban misali  a kan haka, yadda manyan mutane ke shiga, kuma cikin ikon Allah da dagewar da suka yi, sukan shahara a fannin ilimi.      

Mene burinka a rayuwa?

Babban burina shi ne, in cika da imani,  Allah ya shiryi zuri’ata kuma bayan ba ni, wannan Cibiya ta ci gaba da habaka, har illa masha Allahu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: