Connect with us

LABARAI

Babbar Sallah: Yadda Hada-hada Ke Wakana Gabanin Idi A Kasuwar Gwari Ta Mile 12

Published

on

A yanzu haka kwanakin gudanar da bukukuwan sallar idin Babbar Sallar wannan shekara na ta kara kurewa, sannan kuma kasuwannin da a ke sayar da kayan abincin da sauran kayan da a ke sayar da kayan abincin da sauran kayan da a ke amfani da su a wajen gudanar da bukukuwan sallah a yanzu haka su na nan su na cigaba da gudanar da hada-hadar kasuwancin kusa da sallah a duk fadin kasar.

Dangane da wannan al’amarin ne wakilin LEADERSHIP A YAU na jihar Legas ya yi tattaki zuwa wadansu kasuwannin cikin garin Legas, domin shaidawa tare da tabbatar da sanin farashin wadansu kayayyakin da a ke saidawa a wadansu kasuwannin a garin L:egas.

Wakilin namu ya ruwaito ma na cewar, ya shiga kasuwar sayar da kayan miya da ke unguwar Mile 12, kuma ya sadu da shugaba mai kulawa da bangaren kasuwancin tumatiri na kasuwar, Alhaji Abdul Giyasu Rano ta jihar Kano, wanda ya ce, babu shekka kasuwancin tumatiri ya na kara samun cigaba a wannan babbar kasuwar mai albarka ta Mile 12.

Ya kara da cewa, a yanzu haka sababbin kwastomomi su na ta shigowa kasuwar ta Mile 12, domin sayen kayan miya da sauran kayan abinci zuwa garuruwan da su ke bukata.

Sannan kuma ya sada wakilinmu da daya daga cakin jami’ai masu kulawa da farashin kayan miya na kasuwa, Alhaji Dan’audi Kudan, wanda shi kuma ya ce, a yanzu dai a na saida tumatirin Yarabawa na kananan kwanduna ne a kan Naira 800, sai kuma na Hausa kires dubu hudu zuwa dubu biyar. Sai kuma Tumatirin Kamaru dubu bakwai, sai tumatirin Ghana dubu 12.

Jami’in mai kulawa da farashin kayan miya bangaren tumatirin, Alhaji Dan’audi Kudan ya ce, amma su na sa ran samun nasarar ciniki mai tsafta kafin nan da lokacin gudanar da bikin sallah babba mai zuwa.

Ya kara da cewa, da ma farashin gwari haka ya ke; wani lokaci ya yi sama wani lokacin kuma ya yi kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!