Connect with us

LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 1, Da Latata Gona 300 A Bauchi

Published

on

An sake samu aukuwar wani ambaliyar ruwa a yankin Kari wanda yake kan hanyar Bauchi-Maiduguri da ke jihar Bauchi, inda ya kashe ran mutum guda da tursasa ma wasu jama’a da dama kaura daga muhalansu a sakamakon rusa musu gidaje da matsugini, inda a halin yanzu suke gudun hijira zuwa wani makarantar Firamare da sakandari da ke yankin.

Ambaliyar wanda ya lalata muhallai daban-daban a garin Kari da ke karamar hukumar Darazo, hakan ya faru ne a sakamakon ruwa mai karfi da aka yi a ranar Laraba da daddare wanda ya ci gaba da sauka har zuwa ranar Alhamis shekaran jiya, inda ya wuce da gidajen jama’a da dama da gonakansu a wannan yankin.

Mai rikon mukamin shugaban karamar hukumar Darazo, Gara’u Adamu ya shaida hakan a jiya Juma’a a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga wadanda lamarin ya shafa a can yankin nasa.

Shugaban, wanda ya samu wakilci daga babban jami’in gudanarwa na karamar hukumar, Alhaji Ibrahim Ahmed Muhammad, ya shaida cewar akalla gonakai 300 ne suka lalace a sakamakon ruwa mai karfin gaske da aka tafka.

“Muna son mu jawo hankalin iyaye da suke kula sosai da yaransu da su daina kusantar wuraren magudanar ruwa a sakamakon tsananin ruwa da ake tafkawa a ‘yan kwanakin nan,” A fadin shi.

Gara’u ya mika sakon ta’aziyya ga wadanda abun ya shafa, yana mai fadin cewar wannan tsautsayi ne daga Allah, kana ya fadi cewar gwamnatin jihar za ta duba bukatar tallafa musu kan ababen da suka yi asara.

Kauyen Kari dai ya hada magudanar ruwa da kogunai daban-daban a bisa haka ne duk shekara ruwa ke ambaliya a yankunan.

Wakilinmu ya labarto cewar a dai ‘yan kwanakin nan ana samun aukuwar ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na jihar Bauchi, a bisa haka ne ma a kwanakin baya gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana shirinsa na tabbatar da tsaftace magudanar ruwa domin kare jama’a daga ambaliyar ruwa wanda tunin aikin ya fara nisa kamar yadda bincikenmu ya gano.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: