Connect with us

MANYAN LABARAI

Rikicin Kabilanci Ya Janyo Rufe Hanyar Abeokuta Zuwa Legas

Published

on

Wani rikici ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa yan kasuwa a kasuwar Oke-Odo da ke hanyar babban tiin Lagas Abeokua wanda yayi sanadiyar tushewar hanya a yankin.

Ababen hawa da suka doshi hanyar Lagas daga Sando a jihar Ogun da wadanda ke afiya zuwa Abule-Egba daga Oshodi da sauran yankunan jihar sun tsaya cik.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai; cewa rikicin ya fara ne a daren jiya lokacin da yan kasuwa a kasuwar kayan abinci suka fara rigima kan wani lamari da ba a san musababbin shi ba

An tabbatar da cewa lamarin ya kara kamari da safiyar yau Lahadi lokacin da yan kasuwar suka fara kone-kone.

A halin da ake ciki, mun ji cewa rundunar yan sandan Nijeriya a ranar Lahadi, 18 ga watan Agusta, ta yi nasarar takaita rikicin da ya fara a tsakanin Hausa da Yarbawa a wani yanki na jihar Lagas.

Ba a san dalilin barkewar rikicin ba, amma rundunar RRS a wani jawabi da ta saki, tace jami’anta na a kasa domin daidaita lamarin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: