Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Binuwe: Tirela Ta Murkushe Dan Acaba Dauke Da Mace

Published

on

A ranar Talata ce, wata tirela ta murkushe wani dan acaba tare da fasinjansa mace a garin Makurdi babbar birnin Jihar Benuwe. Wakilinmu ya labarta mana cewa, hatsarin wanda ya faru a kan babbar hanyar New Otukpo da ke Makurdi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa ya bayya wa wakilinmu cewa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 8.40 na safe, an kwashe gawarwakin mutum biyun da hatsarin ya rutsa da su.

Har lokacin da a ke tattara wannan rahoton ba a san daga inda tirelan ta taso ba, amma dai kwamandar sashe na hukumar kiyaye hadararruka Aliyu Baba, ya tabbatar da wannan hatsarin. Ya bayyana cewa, an samu nasarar cafke direban tirelan kuma ma har an mika shi ga hannun ‘yan sanda. Sai dai ba a bayyana sunayen wadanda hatsarin ya rutsa da su ba.

An bayyana cewa, jami’an hukumar kiyaye hadararruka sun isa wurin da lamarin ya faru, inda su ka kwashe gawarwakin, yayin da su ka yi kokarin bude hanyar a yankin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!