Connect with us

LABARAI

Sarkin Kano Ya Gargadi ‘Yan Jarida Kan Ba Da Rahotanni Masu Cin Rai

Published

on

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II ya gargadi ‘yan jarida musamman jaridu da su guji rahotanni masu cin rai domin kawai ganin sun siyar da jaridun na su. Ya kara da cewa; ya kamata a ce ‘yan jarida su daina bizne hakikanin sakonni ga masu karatunsu ta hanyar yin kanun labari mai daukar hankali wanda ka iya jawo rikici.

Ya ci gaba da cewa; da yawan manyan mutane na son cewa wani abu dangane da batutuwa amma sun tsoron yadda za a sauya zancen na su zuwa wani abu daban. Sarkin Kano din ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Kano a lokacin da kungiyar manema labarai ta kungiyar ‘yan jarida na Nijeriya reshen jihar Kano suka kai masa ziyara.

Sarkin Kano din ya ce kasarnan na fuskantar tarin matsalolin zamantakewa da na tattalin arzikin kasa wanda ya kamata a ce an bai wa gwamnatin shawarar yadda za ta magance su. Ya ce wanda wannan shawarwarin ne ya kamata ya cika rahotannin ba murguda labarin zuwa wani abu daban ba.

Ya tunatar da ‘yan jaridar cewa; suma fa ‘yan Nijeriya ne da suke fuskantar wadannan matsalolin da ‘yan Nijeiya ke fuskanta a kasarnan, ya ce akwai bukatar su damu da bankado hanyoyin da za a magance matsalolin.

Sarkin Kano din ya jinjinawa manema labarai din inda  ya yi kira gare su da su ci gaba da ayyukansu yadda ya kamata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: